Lalacin gwamnatin Buhari ya sa Tiwita ya bude ofishinsa na Afirka a kasar Ghana ba Najeriya ba – PDP

0

Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa salon mulkin shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ne ya sa kamfanin Tiwita zai bude ofishinsa na farko a Afirka a kasar Ghana maimakon Najeriya.

A Najeriya sama da mutum miliyan 32 ke amfani da shafin tiwita wanda ya fi yawan mutanen kasar Ghana gaba dayanta.

” Saboda haka idan ba lalacin wannan gwamnati ba da yin watsi da matasa da bata basu mahimmanci ba, bai kamata ace wai a kasar Ghana ne Tiwita za ta bude ofishinta na Afirka ba.

Shugaban kamfanin Tiwita, Jack Dorsey ya bayyana cewa ya fi ganin Ghana a matsayin kasa da ke baiwa mutane damar bayyana ra’ayoyinsu da kuma yanayi na siyasa mai nagarta.

Wadannan suna wasu daga cikin dalilan da ya sa zan bude ofishina na yankin Afirka a kasar Ghana.

Share.

game da Author