Wani mafusacin maigida ya burma wa limanin garin Enagi mai suna Allhaji Attahiru Alhassan rodi ya kashe shi, bisa haushin kama shi da ya yi ya na lalata da matar sa a gidan makauta.
Kafafen yada labarai da dama, ciki har da Daily Trust sun ruwaito cewa mijin matar mai suna Umar Jubril mai shekaru 35, ya ce ya kama Liman Alhaji Attahiru mai shekaru 48 a kan gado tare da matar sa a gidan makauta.
An gabatar da Jubril a Hedikwatar ‘Yan Sandan Jihar Neja a ranar Talata inda ya bada bayanin yadda ya kama Liman Attahiru a kan ruwan cikin matar sa, kuma a cikin gidan makwauta.
Ya ce Liman Attahiru ya wuce shi ya shiga gidan da ke makautaka da shi, inda dama ita matar ta sa ta shaida masa cewa za ta zaga ta yi bayan gida a bayan gidan su.
Jubril ya ce yayin da ya ga matar sa ta dade har awa daya ba ta dawo daga bayan gidan da ta ce za ta dan zagaya ta yi ba, sai ya kewaya domin ya nemo ta.
Kewayawar da ya ke yi kuwa sai ya ji muryar ta a cikin gidan makautan su, wato gidan da Liman Attahiru ya shiga kenan.
“Ina shiga cikin gidan, sai na samu Liman Attahiru tsirara a kan mata ta su na lalata. Ban ce masu komai ba, sai na fito, na je na sanar da wani dan uwa na abin da na gani da ido na.” Inji Jubril.
Ya ci gaba da cewa ran sa ya baci matuka a lokacin da Liman Attahiru ya gayyace shi domin su yi sulhu kan lamarin.
“A locakin da mu ke tattaunawa, kowanen mu ya dau zafi, mu ka fara gardama, har na yi kukan-kura na kwace wani rodi daga hannun Liman, na burma masa a wuyan sa.”
Wannan ne silar mutuwar Liman, shi kuma Jubril ya gudu, amma daga baya jami’an ‘yan sanda su ka kamo shi a kauyen Babati da ke cikin Karamar Hukumar Lavun ta Jihar Neja,
Sai dai kuma hasalallun matasan garin Enagi sun yi kokarin kutsawa ofishin ‘yan sandan garin domin yi wa Jubril rubdugu, amma jami’an tsaro su ka gudu da shi zuwa Hedikwatar su ta Neja a Minna.
Kakakin ‘yan sandan Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun ya shaida wa manema labarai cewa wanda ake zargin ya amsa laifin sa cewa shi ya kashe Liminan Attahiru Alhassan, amma a bisa fushin yin lalata da matar sa.
Daga karshe ya ce ana ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da shi kotu da zaran an kammala bincike