Sakataren yada labaran Jam’iyyar PDP Kola Ologbondiyan ya yi kira ga mutane su yi watsi da labaran da ake yadawa wai jam’iyyar PDP ta kori wasu daga cikin jiga-jigan ‘ya’yan ta biyu, Rabiu Kwankwaso da Babangida Aliyu.
Kola Ologbondiyan ya ce babu wanda ya isa ya kore su ba tare da sa hannun uwar jam’iyyar ba.
” Ba a kori Kwankwaso ba, wadannan maganganu basu da tushe, kuma ba gaskiya bane. Ina kira ga ya’yan jam’iyyar PDP su yi watsi da duk wani takarda da aka fitar kan haka.
Haka shi tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu, da aka yada cewa wai PDPn mazabar sa ta dakatar da su shi daga jam’iyyar.
Jam’iyyar ta ce gaba dayan su na nan daram a PDP bau wanad ya kore su ko ya dakatar da su.