A ranar Talata ne shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da canja kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar cutar korona PTF zuwa kwamitin shugaban kasa kan tsare-tsare da kula da ayyukan Korona.
Shugaban kwamitin kuma sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya sanar da haka ranar a taron da kwamitin ke yi da manema labarai a Abuja.
“Tun a ranar 31 ga Maris 2021 ne wa’adin aikin kwamitin PTF ya cika sai dai kuma bayan mika wa shugaban kasa rahoton ayyukan da muka yi da yin sallama da aikin sai ya canja wa kwamitin suna ya maida ta kwamitin shugaban kasa kan tsare-tsare da kula da ayyukan Korona.
“kwamitin shugaban kasa kan tsare-tsare da kula da ayyukan Korona zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Afrilu 2021.
Idan ba a manta ba shugaban ƙasa Buhari ya kafa kwamitin PTF ranar 9 ga Maris 2020 domin tsara hanyoyin dakile yaduwar cutar korona a kasar nan.
Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ne aka nada shugaban kwamitin sannan Kodinatan kwamitin kuma aka nada Sani Aliyu.
Sauran mambobin kwamitin sun hada da ministan lafiya Osagie Ehanire, ministan yada labarai Lai Mohammed, ministan muhalli Muhammad Mahmood, karamin ministan lafiya Olorunnimbe Mamora, shugaban hukumar dakile yaduwar cututtuka NCDC Chikwe Ihekweazu da shugaban fannin dakile yaduwar cututtuka na kwamitin PTF, Mukhtar Muhammad.