Kungiyar CAN ta umarci Kiristoci su yi turereniyar shiga siyasa

0

Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta karfafi guyawun Kiristocin Najeriya cewa su yi rige-rigen shiga siyasa, yayin da zaben 2023 ke karatowa.

CAN ta ce wannan ce kadai hanyar da za a rika hana wadanda ba su cancanta ba su yi mulkin Najeriya.

Shugaban CAN na Kasa Samson Ayokunle ne ya bayar da wannan shawara a ranar Talata, a lokacin da ya ke jawabi mai take, ‘Halin Da Kasa Ke Ciki’, a Cocin VLBC, a garin Abeokuta.

Ya nuna damuwa matuka dangane da hanlin da kasar nan ke ciki. Sannan kuma ya kalubalanci Shugaba Muhammdu Buhari ya kakkabe muggan makaman da ke hannun muggan mutane a fadin kasar nan.

Ayokunle ya roki Buhari ya gaggauta daukar kwakkwaran mataki kafin “abubuwa su gagare shi dakilewa”, ya kuma kara da cewa lokaci fa ya yi da gwamnati za ta daina daukar masu fada mata gaskiya abokan gabar ta.

“Ina tausaya mana dangane da yadda shugabannin mu ke irin dabi’un da su ke yi wai don su na kan mulki.” Inji Shugaban CAN.

“Amma an wayi gari a yanzu duk wani mai fada wa gwamnatin nan gaskiya, kallon abokin gaba ake yi masa. Don ka na cikin Fadar Shugaban Kasa a Aso Rock, sai me? Ai hakan ba ya na nufin ka fi ni zama cikakken dan Najeriya ba.

“Rashawa da cin hanci su ne ciwon sankarar da ke lalata kasar nan. Ida ana so a kakkabe cin hanci da rashawa a Najeriya, to dole sai Kiristoci sun shige gaba.”

Sannan kuma ya nuna cewa akwai bukatar da sake nazarin kundin tsarin mulkin Najeriya, domin a shigar da dimokradiyyar mu ta cikin gida, maimakon kacokan mu rika dogaro da tsarin dimokradiyyar da aka dauko daga wasu kasashen duniya.

Ya yi korafin cewa wasu matsolin da Najeriya ke fuskanta sun hada da rashin ilmi wajen zakulo bayanan sirri kan tsaron al’umma.

A kan haka, sai Ayokunle ya nanata cewa ya zama dole a kirkiro ‘yan sandan jihohi, domin cewar sa, gwamnatin tarayya ce ke bayar da kofa har matsalar tsaro ke yin kaka-gida a yankunan kasar nan.

Share.

game da Author