Wasu mahara da ba a san ko su wane ba, sun kai hari da manyan bindigogi rokoki a kan gidan Gwamna Hope Uzodinma da ke kauyen su, can a Omuma Oru, a Jihar Imo.
Ba Gidan Gwamnatin Jihar Imo aka kai wa harin ba. An kai harin ne gidan da gwamnan ya mallaka da ya gina a garin su.
Maharan sun kai harin a yau Asabar da safe, misalin karfe 9 na safiya.
Sai dai har yanzu ba a san adadin yawan wadanda aka kashe a harin da aka kai wa gidan ba.
Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Imo, Declan Emelumba ya tabbatar da an kai harin, amma ya ce jami’an tsaro sun kori maharan.
“Wasu mahara dauke da manyan bindigogi, a cikin jerin gwanon motoci 15, wajen karfe 9 na safiyar yau Asabar, sun kai hari a gidan Gwamna Uzodinma da ke garin da aka haife shi.
“Sun yi kokarin banka wa gidan wuta, domin har da tsoffin tayoyi cike da mota kirar ‘tipper’ su ka je.
“Sun yi arangama da jami’an bijilante da jami’an tsaron gidan. Amma an samu asarar rayukan wasu jami’an tsaro biyu. Daya Sajan na ‘Yan Sanda, daya kuma dan bijilante.”
Emelumba ya bayyana cewa sun hakkake wannan hari da aka kai ya na da nasaba da siyasa.
Jihar Imo kamar sauran jihohin Kudu maso Gabas, ta afka cikin rikicin fa ya kazanta sosai, tun bayan harin karya kofar gidan kurkukun Owerri da aka fitar da daurarru sama da 1,800.
An kuma kai wa ofisoshin ‘yan sanda da dama hari a jihar.