KUDU TA DAGULE: Dandazon ‘yan iska sun banka wa Babbar Kotun Tarayya wuta a Ebonyi

0

Da jijjifin safiyar Talata ce wani dandazon matasa masu tarin yawa su ka banka wa Babbar Kotun Tarayya da ke Abakaliki wuta.

Garin Abakaliki can ne babban birnin Jihar Ebonyi, daya daga cikin jihohin kabilun Igbo, inda ake yawan tashe-tashen hankulan kone kadarorin gwamnatin tarayya.

Babbar Kotun ta Tarayya, wadda ke kan babban titin Abakaliki zuwa Enugu, an banka mata wuta da jijjifin safiya, inda dandazon matasa su ka rika wurga mata bama-bamai na fetur.

Wutar ta lashe bangaren dakin karatu na babbar kotun da kuma bangaren jami’an tsaron kotun.

Rahotanni sun tabbatar da cewa jami’an kashe gobara sun isa cikin gaggawar da su ka kashe wutar kafin ta kai ga lashe sauran bangarorin kotun.

Kakakin Yada Labarai ta ‘yan sandan Ebonyi, Loveth Odah, ta bayyana wa wakilin mu cewa ba a samu asarar rayuka ko daya ba.

Ta ce wadanda su ka kai farmakin banka wa Babbar Kotun Tarayya din wuta, dandazon matasa ne masu tarin yawa.

Ana ganin an kai wa kotun hari ne domin a kawo cikas ga gwamnati wajen gudanar da wasu ayyuka na ta.

Wannan ne hari na baya-bayan nan a ci gaba da hare-haren da ake kai wa ma’aikatun gwamnatin tarayya, ofisoshin jami’an tsaro da kuma jami’an tsaron su kan su, a jihohin Kudu-maso-Gabas, inda tashe-tashen hankula ke kara dagulewa.

Share.

game da Author