Ku kare kanku daga ‘Yan bindiga, amma kada ku karya doka – Gwamnatin Zamfara

0

Kwamishinan watsa labarai na jihar Zamfara, Ibrahim Dosara ya umarci mutanen jihar Zamfara su kare kansu daga’ Yan bindiga idan suka far musu sai da ya ce abi kamar yadda doka ta gindaya.

” Gwamnati ta amince mutane su fito su kare kan su daga hare-haren ‘yan bindiga idan suka far musu. Sannan kuma gwamnati ta gargadi masu gidaje dake baiwa’ yan bindiga hayan gidaje a kauyuka da su shiga taitayin su domin duk wanda aka samu yayi haka daga yanzu za a rusa gidan sa.

Dosara ya kara da cewa kamar yadda Channels TV ta ruwaito, an kama wasu yan bindiga da masu aika musu da bayanan sirri sama da talatin kuma an maka su a kotu.

Akarshe ya gwamnati ta yi kira ga ‘yan bindiga, su amshi shirin sulhu na gwamnatin jihar su ajiye makamai.

Jihar Zamfara, Katsina da Kaduna, na saga cikin jihohin da hare-haren yan bindiga da garkuwa da mutane yayi tsanani a yankin Arewa Maso Yamma.

Duk da cewa gwamnatocin Katsina da Zamfara sun amince da ayi sulhu da yan ta’adda amma kuma kamar an basu damar ci gaba da kai hare-hare ne da yin garkuwa da mutane. Mahara da yin garkuwa da mutane sai ya kara yin tsanani a jihohin.

Jihar Kaduna ma a jere ana kwashe daliban makaranta wanda har yanzu suna tsare a hannun yan bindiga bayan kashe wasu da su ka yi.

Share.

game da Author