Kotu ta daure magidanci saboda satar wutan lantarki a Kano

0

Kotun majistare dake unguwar Hajji Camp, Kano, ta aika da wani mazaunin unguwar Janbulo, Mu’ammar Aliyu, gidan gyaran hali bayan samunsa da laifin satar wutan lantarki.

Kotun ta kama Aliyu da kaninsa maisuna Suleiman Aliyu wanda a yanzu haka ya arce ba a san inda ya ke ba. Sun kwankwadi adadin wuta mai yawan 5,500 wadda kudinsa ya kai sama da N100,000

Kamfanin raba wutar lantarkin ta KEDCO tayi karar magidancin da kaninsa, suna zarginsu da satar wutar harna wata 15.

Maimagana da yawun Kamfanin raba wuta to KEDCO Ibrahim Shawai, ya shaida wa manema labarai cewa Alkali Sakina Yusuf ta ce laifin ya sabawa dokokin panel court ta Kano sashe 97 da 286 da kuma sashe na 2

Alkali Yusuf ta umarci wadanda ake kara dasu biya kamfanin na KEDCO tsabar kudi N101,250.00 ko kuma suyi zaman gidan gyaran hali na shekara daya.

Zasu kuma biya N20,000 kudin tara ko kuma zaman gidan gyaran hali na wata shida inji kotu.

Ba a jihar Kano ba, a lokutta da dama ana kai ruwa rana tsakanin magidanta da kamfanonin wutan lantarki.

A inda wasu da dama ke ganin ana cajar su kudin wuta masu yawan da ba su ma sha wannan wuta ba.

A dalilin haka suke satar wutar su sha yadda suke so ba tare da sun biya ko sisi ba.

Wannan dalili ya sa suma hukumomin ke farautar irin wadannan mutane domin a hukunta su.

Share.

game da Author