Saudiyya ta bada sanarwar cewa ba za ta bari maniyyata masu zuwa Umra ko zirga-zirgar hada-hada daga wasu kasashe 20 shigar ta ba, idan ta bude damar sake zirga-zirgar jirage cikin kasar daga ranar 17 Ga Mayu.
Kasashen 20 dai sun hada da Argentina, UAE, Germany, Amurka, Indonesia, Ireland, Italy, Pakistan, Brazil, Portugal, UK, Turkey, South Africa, Sweden, Switzerland, France, Lebanon, Egypt, India da Japan
Idan aka bude tashoshin jiragen kasar, za a ci gaba da hana wadannnan kasashe 20 shiga Saudiyya a matsayin kwakkwaran matan haka mummunar illar cutar korona a Saudiyya tun daga ranar 3 Ga Fabrairu.
Wannan haramci ya hada da dukkan wani fasinga ko dan wace kasa ne da jirgin su ya yada zango a wadannan kasashe, to ba za a bari idan sun taso ya sauka Saudiyya ba. dole zai kasance ya isa Saudiyya a cikin kwanaki 14 da su ka rattaba adadin neman bizar shiga kasar da ya nema.
Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan Saudiyya ce ta yi wannan sanarwar cewa wadanda ba ‘yan kasar Saudiyya ba da jami’an diflomasiyya da jami’an lafiya da iyalan matafiya daga wadannan kasashe 20 duk an haramta masu shiga Saudiyya
Jaridar Arab News da Kamfanin Dillancin Labarai na AFP duk sun ruwaito wannan labari.
cewa adadin wadanda cutar korona ta kashe a kasar sun karu zuwa mutum 6858.
Ma’aikatar Lafiyar kasar ta ce mtum 408,038 ne su ka kamu, inda mutum 9,818 ke kwance magashiyan sakamakon kamuwa da korona, yayin da ake ci gaba da dankara wa jama’a rigakafin korona a kasar.
Idan ba a manta ba, Saudiyya ta ce babu wanda zai yi Umra ko aikin Hajjin 2021 sai an yi masa rigakafin korona.