Najeriya za ta karbi maganin rigakafin cutar korona na Johnson & Johnson (J&J) guda miliyan 29.8 daga wajen AU.
Shugaban hukumar cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko ta ƙasa NPHCDA Faisal Shu’aib ya sanar da haka a taron da kwamitin shugaban kasa kan tsare-tsare da kula da ayyukan Korona ta yi da manema labarai ranar Litini a Abuja.
Shu’aib ya kuma ce Nageriya na sa ran karban sauran maganin rigakafin Oxford-AstraZeneca daga hannun asusun COVAX a cikin watan Mayu ko kuma Yuli.
Ya ce zuwa yanzu Najeriya ta kammala yi wa mutane allurar rigakafin korona karo na farko da maganin rigakafin na Oxford-AstraZeneca.
Ya ce hakan ya faru ne bayan gwamnati ta karbi kwalaben maganin rigakafin guda miliyan 3.94.
Rigakafin Korona
Shu’aib ya bayyana cewa daga watan Maris zuwa Afrilu an yi wa mutum 1,175,285 allurar rigakafin korona a kasar nan.
Hakan ya nuna cewa an yiwa kashi 58.4% na adadin yawan mutanen da ya kamata a yi wa rigakafin a kasar nan.
Ya ce a yanzu haka jami’an lafiya na nan na yi wa mutane allurar rigakafin a duk jihohin kasar nan.
Shu’aib ya koka da yadda duniya ke fama da karancin maganin rigakafin cutar.
Ya ce domin gudun kada maganin ya Kare kar-kaf ya sa gwamnati ta dakatar davyi wa mutane allurar rigakafin.
Duk da haka Nageriya na nan akan bakan ta na yi was miliyan 109 allurar rigakafin cikin shekara biyu.
Gwamnati ta umurci jami’an lafiya da su yi wa masu shekaru 18 zuwa sama allurar rigakafin korona a kasar nan.