Kungiya mai zaman kanta ‘Victims Support Fund (VSF)’ ta bada gudunmawar na’urorin yin gwajin korona guda 60,000 ga hukumar kula da dalibai masu yi wa kasa hidima (NYSC).
Kungiyar ta damka wadannan kaya ga kwamitin shugaban kasa kan tsare-tsare da kula da ayyukan Korona PSC ranar Litini.
Shugaban kwamitin dakile yaduwar cutar na kungiyar VSF Toyosi Ogunsiji ta bayyana cewa wannan shine babban gudunmawar da kungiyar ta yi wa gwamnatin Najeriya tun bayan bullowar Korona.
Ogunsiji ta ce kudin wadannan kaya zai kai Naira miliyan 210.
Ta ce tallafin da kungiyar ta yi zai taimaka wa gwamnati wajen shirye-shiryen da take na bude sansanonin horas da dalibai masu yi wa kasa hidima ranar 17 ga Mayu 2021.
“Kungiyar VSF za ta ci gaba da mara wa gwamnati baya wajen ganin an kau da cutar korona a kasar nan.
Discussion about this post