KASHE-KASHE: Yadda ‘yan bindiga suka kashe mutum sama da 83 a cikin kwana daya a jihar Zamfara

0

Duk da tsayawa tsayin daka da dagewa da gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya yi cewa sulhu ne ya fidacewa gwamnati ta yi da mahara, wanda kuma hakan ya saka agaba, ga dukkan alamu Sulhu bai haifar wa jihar Zamfara da mai ido ba.

A ranar Alhamis ake sa ran za ayi jana’izn mutane sama da 80 da ‘Yan bindiga suka kashe a fadin jihar, tun daga Gusau babban birnin jihar.

‘ Yan bindiga sun rika bi kauyuka kauyuka suna kashe mutane yadda suke batare da jami’an tsaro sun taka musu birki ba.

Rahotanni sun nuna cewa da yawa daga cikin wadanda aka fi kashe matasa ne da suka nemi yin fito-na-fito da maharan a kokarin kare kauyukan su.

Mazauna garuruwan da kauyukan jihar Zamfara na ta yin kaura zuwa wasu garuruwa domin samun mafaka daga hare-haren ‘Yan bindigan.

Kauyukan da’ Yan bindigan suka afkawa sun hada da Gobirawa, Gora, Rini da Madoti Dankule a kananan hukumomin Maradun da Bakura

Sannan akwai ‘Yar Doka, Kango, Ruwan Dawa, Madaba, Arzikin Da and Mairairai, wanda duk suna karkashin karamar hukumar Gusau ne.

Karanta labarin na baya

Akalla an kashe mutum 20 a ranakun Alhamis da Juma’an makon jiya, a wasu hare-haren daukar fansa tsakanin ‘yan bindiga da ‘yan sa-kai a Karamar Hukumar Maru, Jihar Zamfara.

Mazauna yankukan karkarar da abin ya faru su da jami’an asibti sun tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa wadanda aka kashe din sun kai mutum 20.

Wakilin PREMIUM TIMES ya yi tattaki har zuwa yankunan da lamarin ya faru.

Mazauna yankunan sun shaida wa wakilin mu cewa ‘yan bindiga sun kai hari a ranar Alhamis su ka kashe mutum uku a Ruwan-Tofa.

Washegari a ranar Alhamis kuma mazauna garin wadanda ‘yan bijilante ne, su ka kai harin daukar fansa a wata kasuwar shanu a Dansadau, har su ka kashe Fulani 16, su ka bar wasu mutum biyar kwance cikin jini.

Tuni dai Gwamnatin Jihar Zamfara ta soke duk wasu ‘yan bijilante a jihar, saboda Fulani na kai kukan cewa ‘yan bjilante na kashe wadanda ba su ci ba, ba su sha ba.

Wani mazaunin yankin da abin ya faru, wanda ya roki a sakaya sunan sa, ya bayyana wa wakilin mu daga cikin mutum uku da aka kashe a Ruwan Tofa sun hada wani kasaitaccen dan bijilante ne mai suna Sanusi Manu.

Sannan kuma PREMIUM TIMES HAUSA ta ji cewa mahaifin Sanusi Manu mai suna Alhaji Maiburkasa, shi ma ‘yan bindiga nesu ka kashe shi a shekaru bakwai da suka wuce.

Sanusi ya shiga aikin bijilante ka’in da na’in, tun bayan bindige mahaifinsa shekaru bakwai da auk gabata, inda ya shahara sosai wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’ar yankin Dansadau.

Jama’a sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa kisan da ‘yan bindiga su ka yi wa Manu ya sa ‘yan bijilante fusata su ka kai hari cikin gungun Fulani a tsakiyar kasuwar Dansadau, a bangaren masu cinikin shanu, a ranar Juma’a da ta gabata.

Su kuma Fulani ‘yan binidiga a yammacin Juma’a sun sake kai hari a garin Mai-Tukunya domin daukar fansar kisan kan mai uwa da wabi da aka yi wa Fulani a kasuwar Dansadau.

A Mai-Tukunya sun kashe mutum daya mai suna Nasiru Habibu, sun ji wa mutum hudu rauni.

Sannan kuma majiya ta ce sun saci shanu za su kai 100.

Kisan daukar fansa ya ci rayuka 20 a Zamfara

Jami’an kiwon lafiya a Asibitin Dansadau sun shaida wa wakilin mu cewa an kai masu gawarwaki 16 su na ajiye a dakin ajiye gawawwaki cikin asibitin.

“Daga cikin wadanda ‘yan bijilante su ka kashe a kasuwa, akwai wani shugaban Fulani mai suna Batume Saulawa. Kuma jami’an tsaro sun rako Fulani zuwa asibitin domin duba gawarwakin dangin su da aka bindige a kasuwar Dansadau.”

Share.

game da Author