Mahara sun kashe matafiya tara sannan sun yi garkuwa da wasu da dama a jihar Kaduna.
Wannan hari ya auku ne a hanyar Kachia inda maharan suka bude wa wata babbar mitar itace dana fasinja wuta.
Jihar Kaduna na daya daga cikin jihohin Arewa dake fama hare-haren ‘yan bindiga a kasar nan.
Kwamishina tsaron jihar Samuel Aruwan ya bayyana sunayen wadanda maharan suka kashe kamar haka;
Alfred Makinde, wanda shine direban Bas din, Abdulrahman Dela, Dauda Adamu, Umar, Dauda da Abdulrasheed Musa. Sannan kuma Murtala Ibrahim, Ali Manager da Abdullahi, duk suna asibiti ana duba su.
Sannan kuma a wani harin na daban mahara sun afka wa rugan Fulani Inlowo inda suka kashe wani Ibrahim Haruna sannan suka sace sanu 180.
Haka kuma a kauyen Akilbu, maharan sun bude wa motar wasu matafiya inda suka ji wa mutum biyu rauni suka.
Daya daga cikin su ya rasu a asibiti.
Discussion about this post