Gwamnatin Jihar Zamfara ta kafa sabuwar dokar hana bunmmburutun man fetur a yankunan da aka kashe sama da mutum 90 a jihar cikin wannan makon.
Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Zamfara, Ibrahim Dosara, ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar, a ranar Asabar.
Ya ce an kafa dokar ce domin a hana sayar da fetur barkatai a yankunan ta yadda hakan zai hana ‘yan bindigar cikin daji samun fetur a saukake da su ke zuba wa baburan da su ke amfani da su wajen kai hare-hare.
Yankunan da wannan doka ta shafa sun hada da garuruwan Wanke, Magami, Dansadau, Dangulbi, Dankurmi, Bindin, Munhaye, Kizara, Kunchin, Kalgo da kewayen su.
Sannan kuma sanarwar ta ce an kafa dokar ba a san ranar janye ta ba, har sai yadda hali ya yi.
Kwamishina Dosara ya kuma umarci masu gidajen mai a garuruwan cewa kada su kara sayarwa masu galan, jarka ko wani irin mazubi.
Ya ce an amince kawai su rika sayar da fetur a motocin da aka tuka aka shiga da su gidan mai.
An umarci jami’an tsaro su damke duk wani wanda ya karya wannan doka.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin mummunan kisan sama da mutum 90 da aka yi a kewayen Magami, cikin Karamar Hukumar Gusau.
Discussion about this post