Jama’atu Nasril Islam ta karyata kwafen takardun da ta ce na bogi ne, wadanda su ka danganta Ministan Sadarwa Isa Pantami da kisan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Patrick Yakowa.
JNI ta yi wa jami’an tsaro tsokacin cewa su gaggauta binciken salsala da tushen da kwafen takardar ya fito.
Takardar wadda ta nuna cewa an yi ganawar sirri a cikin Yuli, 2010 tsakanin JNI bisa shugabancin Pantami, ta nuna wai sun tsara makarkashiyar yadda za su kashe Yakowa.
Sakataren JNI Khalid Aliyu ya bayyana cewa wannan zargi abin takaici ne kuma abin bakanta rai.
Sannan kuma ya nuna mamakin yadda za a ce wai an yi zaman sirrin kashe wani, har aka rubuta kulle-kullen kisan, aka adana a takarda.
Aliyu ya ce Pantami bai taba zama shugaba ko jagora na JNI a kasa ko a jiha ba.
“Me zai kai a hada jihohin da ke shiyya daban-daban a wurin taron sirrin?'”
“Idan Musulmai sun tsani Yakowa, ya aka yi ya yi nasara a zaben 2012 a jihar da Musulmai sun fi yawa? Kuma kwanan nan aka zabi gwamna da mataimaki duk musulmai a jihar?”
Aliyu ya ce kakafen da su ka watsa takardun na bogi, sun yi ne kawai domin wasa da hankulan ‘yan Najeriya, a kuma a hana mutane zaman lafiya a kasar nan.
Tuni dai Kungiyar Kiristoci ta Kasa CAN da Majalisar Kolin Musulunci ta Najeriya, NSCIA. su ka bayyana cewa kwafen takardun na bogi ne.
Discussion about this post