Hukumar Zabe Mai Zaman ta Kasa (INEC) ta fara horaswa da bitar sanin makamar aiki ga jami’an ta da ke shugabantar harkar zabe a jihohi 36 da Gundumar Birnin Tarayya a kan hanyoyin yawaita rumfunan zabe.
Babban Kwamishina a hukumar, Farfesa Okechukwu Ibeanu, shi ne ya bayyana haka a ranar Juma’a a wajen taron bitar kwana biyu da aka shirya wa jami’an a Abuja.
Ya ce an shirya taron bitar ne domin a Kara wa jami’an ilimi kan KoKarin da ake yi na mayar da Kananan wuraren kada kuri’a (voting points) zuwa rumfunan zabe a dukkan fadin kasar nan.
Ibeanu, wanda shi ne shugaban Kwamitin Ayyukan Gudanar da Zabe a hukumar, ya ce taron bitar ya na da muhimmanci wajen aiwatar da hanyoyin da za a bi a fadada rawar da masu jefa kuri’a za su taka a harkokin zabe a nan gaba.
Ya kara da cewa horaswar wani muhimmin aiki ne wajen cimma manufar wata tafiya wadda aka fara ta watanni kadan da su ka gabata.
Ya bayyana cewa akwai bukatu a rubuce har 10,092 da aka kai wa hukumar na samar da rumfunan zabe a fadin Kasar nan.
Ya ce, “Damar samar da rumfunan zabe ga masu zabe ya na ta raguwa kuma okarin da ake yi na yawaita su bai samu nasara ba saboda hukumar ba ta yi aiki da dabarar da ta dace ba a kan hakan.
“Don haka ake yin sabon kokarin fara tuntuba tare da aiki da masu ruwa da tsaki a fadin kasar nan domin su amince a warware matsalar wadda ta shafi tsarin zaben a shekaru 25 da su ka gabata.”
Ibeanu ya ce a wajen yin hakan an fito da shawara to amma akwai bukatar a aiwatar da shawarar domin a cimma muradi.
“Don a tabbatar da an bi shawarar a yadda ta ke, tilas ne a samar da isasshen horo ga jami’an da ke gudanar da zabe wadanda su ne shugabannin harkar zabe a dukkan jihohin, wadanda su ne za su aiwatarwar da shirin.
“Burin taron bitar shi ne ya tabbatar da cewa an ilmantar da su kan hanyoyin da ake so a bi wajen gudanar da aikin.”
Ibeanu ya Kara da cewa ana sa ran shugabannin aikin za su maimaita horaswar a jihohin su ga jami’an da ke yankunan kananan hukumomi.
Ya ce ana so a kammala aikin horaswar kafin a fara aikin yi wa masu zabe rajista a ranar 28 ga Yuni.
Ibeanu ya ce INEC ta na aiki domin ta magance matsalolin da ke kawo cikas ga shigar masu zabe cikin tsarin zabe kafin a yi manyan zabubbuka na Kasa.
Shi ma a nasa jawabin, Babban Kwamishina na INEC kuma Shugaban Kwamitin Wayar Da Kan Masu Zabe da Yada Labarai, Mista Festus Okoye, ya ce samar da rumfunan zabe zai samar da damarmaki masu yawa ga sababbin masu yin rajista ta yadda za su samu rumfunan zabe cikin sauKi.
Okoye ya tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa INEC za ta ci gaba da tuntubar Majalisar Tarayya domin a gaggauta aikin yi wa Dokar Zabe garambawul.
A cewar sa, wannan zai sa a shigar da sababbin tsare-tsare da za su inganta shigar da masu zabe cikin tsarin a kasar nan.