Hukumar Sojojin Sama ta bayyana cewa ta kaddamar da binciken zargin yadda sojojin sama su ka yi wa sojojin kasa ruwan wuta a bisa kuskure, a Jihar Barno.
Sojojin na sama sun bayyana haka ranar Litinin biyo bayan rahotannin da ake samu cewa sun yi wa sojojin kasa ruwan wuta har sun kashe soja 20 a wani farmaki ta sama a Jihar Barno.
Wannan farmaki da kisan sojojin sama 20 ana zargin ya faru a garin Mainok, inda Boko Haram su ka ragargaza wani sansanin sojoji a ranar Lahadi.
Harin da Boko Haram su ka kai ne ya sa aka gaggauta kiran sojojin sama, domin su je su kai wa sojojin sama dauki a Mainok.
A bayanin da Hukumar Sojojin Sama ta fitar a shafin ta twitter, ta bayyana cewa ta fara binciken lamarin, kuma za ta sanar da jama’a abin da ake ciki da zarar an kammala bincike.
“NAF na sanar da jama’a cewa ana binciken wannan rahoto da ake ta yadawa kuma da zaran an kammala bincike, za a sanar wa jama’a dukkan abin da bincike ya tabbatar.
Ba Wannan Ne Karo Na Farko Ba:
Ba wannan ne karo na farko ba da sojojin sama ke tabka kuskure su na kai hare-hare inda ba cikin Boko Haram ba.
Cikin shekarar 2017 sojojin sama sun kai hari ta jirgin yaki, amma su ka tabka kuskuren jefa bam a cikin sansanin ‘yan gudun hijira a Rann, cikin jihar Barno, har su ka kashe mutum 234.
A lokacin har Shugaban Karamar Hukumar Kala-Balge ta Jihar Barno, inda garin Rann ya ke, Babagana Malarima, ya tabbatar da cewa tabbas an rufe gawarwaki 234 a Rann, bayan harin fa jirgin yakin Najeriya ya kai a sansanin gudun hijira bisa kuskure, a ranar 17 Ga Janairu, 2017.