Hukumar kare hakkin ‘dan Adam ta kasa (NHRC) reshen jihar Kano ta bayyana cewa ta saurari kararrakin cin zarafi guda 276 daga watan Janairu zuwa Maris 2021 a jihar.
Kodinatan hukumar Shehu Abdullahi ya sanar da haka a hira da yayi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ranar Laraba a garin Kano.
Abdullahi ya ce daga cikin kararraki 276 hukumar ta kammala gudanar da bincike akan kararraki 203. Yanzu hukumar na aiki akan 73 da suka rage.
Hukumar ta fi sauraren kararrakin yin fyade, sai rashin kula da Yara, cin zarafin yara kanana da sauran su.
Bayan haka Abdullahi ya ce hukumar za ta hada hannu da masu ruwa da tsaki da fannin Shari’a domin kawo karshen wannan matsala.
Ya ce hukumar za ta gudanar da taro na musamman a kauyuka domin wayar da kan mutane sanin illar dake tattare da cin zarafin wani da inda za su na ruka kai koke-koken su domin a share musu hawaye.
Idan ba a manta ba PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda yan sanda suka ceto wata yar shekara 15 a kwatas din Darerawa dake karamar hukumar Fagge wanda iyayen ta suka garkameta a wani dake har na tsawon shekara 10 bata fita ko nan da can ba.
Iyayen Aisha sun kulle ‘yarsu a daki tun tana da shekaru biyar da haihuwa ba tare da tana samun kulawa ba.
Rundunar ‘yan sun Kai Aisha asibiti sannan mahaifiyar Aisha Rabi na tsare a ofishin ‘yan.
Mahaifin Aisha Mohammed ya tsere.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Abdullahi Kiyawa ya ce fannin gurfanar da masu aikata laifuka irin haka za ta ci gaba da gudanar da bincike.