Hukumar NDLEA ta kama hodar Ibilis mai nauyin giram 140 a filin jirgin saman Abuja

0

Hukumar Hana Sha da Fataucin Muggan Kwayoyi (NDLEA) ta kama hodar ibilis mai nsuyin giram 140 da aka boye a gunkin ‘Mary’ wanda ake inkari da ita ce mahaifiyar Yesu.

Darikan Katolika na amfani da gunkin Mary mahaifiyar Yesu wajen yin adu’o’i domin a wurin su Mary ita ce ta haifo mai ceton su.

Sai dai wannan karon wasu kangararrun mutane sun dirka wa gumakan Mary din kwayoyi domin yin safarar su zuwa kasashen waje.

Hukumar NDLEA ta kama gunkin a tashar jiragen saman Abuja a hanyar waske wa da su kasar Philippines.

Shugaban yada labarai na hukumar Femi Babafemi ya sanar da haka ranar Asabar a Abuja.

Babafemi ya ce hukumar ta kama hodar ibilis mai nauyin giram 500 a cikin wata mota da za a ketara da ita zuwa kasar Canada.

Ya ce hukumar ta kama wiwi mai nauyin kilo gram 3.1 da aka boye a cikin kayan kanshi sannan da kilogiram daya na wiwi da aka boye a cikin ganyayyakin maganin gargajiya.

Wadannan kwayoyi duk za a kai su kasashen waje ne.

Bayan haka NDLEA ta kama wasu mutane 31 da kwayoyi masu nauyin kilogiram 276 a jihar Ondo.

Wiwi kilogram 74.285, gram 267 na wasu miyagun kwayoyin da “skuchies’’ wato zoborodo da aka hada da wiwi, tramadol da ethanol na cikin miyagun kwayoyin da aka Kama a hannu wadannan mutane.

Daga nan kuma hukumar ta kama wasu muggan kwayoyin masu nauyi kilogiram 62.150 a garin Oron da Uyo jihar Akwa Ibom.

Shugaban hukumar Obot Bassey ya ce sun Kama mutum hudu da ake zargi da hannu wajen safarar wadannan muggan kwayoyin.

Share.

game da Author