Kakakin rundunar Hisbah ta jihar Kano, Lawal Ibrahim ya bayyana wa Kamfanin dillancin Labarai cewa jami’an Hisbah sun kama wasu mata biyar da maza uku suna warbar abinci a cikin watan ramadan.
An kama wadannan mutane a unguwannin Tudun Murtala dake karamar hukumar Nasarawa da unguwar Hudebiyya, a sharada, jihar Kano.
Kibiya ya ce makwauta ne suka kawo karar wadannan matasan suna cin abinci da gangar.
Hukumar ta ce za ta cigaba da farautar irin wadannan mutane domin hukunta su.