Hisbah a jihar Bauchi ta bayyana cewa zata kirga karuwan dake jihar domin ta sanin yawan su.
Kwamishinan Hisbah Malam Aminu Balarabe-Isah ya fadi haka a wani taro a jihar Bauchi.
Balarabe-Isah ya ce gwamnati za ta kirga yawan karuwan dake jihar ne a wayar musu da kai da karantar dasu illolin dake tattare da sana’ar da suke yi.
Ya kuma ce gwamnati a shirye take domin horas da karuwan sana’o’in hannu da basu jarin yin sana’a domin zama masu cin gashin kansu ta hanyar da ya fi dacewa.
Bayan haka Balarabe-Isah ya ce sakamakon binciken da kungiyar Hisbah ta gudanar a jihar ya nuna cewa cin zarafin da ake yi wa karuwan tun suna yara, kiyayyar da iyayensu suka nuna musu, rashin ilimin boko, talauci na daga cikin matsalolin da ke ingiza mata fadawa cikin wannan sana’a na karuwanci.
Ya ce gwamnati za ta daidaita tsakanin irin wadannan mata da iyayensu sannan ta yi wa duk matan da ta fitar da miji aure.
Daya daga cikin karuwan da suka halarci taron Hafsatu Azare ta shaida cewa za ta daina wannan muguwar sana’a idan har gwamnati ta cika duk alkawaran da ta dauka a wannan taro.