Ba mace ba, kai ko Kartau Sarkin Noma ne ke noma kayan miya a filin gonar da ya kai fadin illin kwallo 20, to ya zama abin kwatance.
Yinka Adesola wata mata ce da ta shahara a fannin noma kayan miya a fadin gona mai hekta 20, wato daidai da fadin filin kwallo har 24, a Jihar Oyo. Yinka na noma hekta 12, kowane wata hekta daya, inda ta ke noma kayan miya iri-iri har kala goma. It ace noman barkono da sauran nau’ukan kayan miya da sinadaran kara wa miya kamshi da gardi da zaki.
“ Za ku yi mamakin jin yadda na ke noma na. Ina da filin noma hekta 20, amma duk shekara hekta 12 na ke nomawa. Kuma duk wata hekta daya na ke nomawa. Idan na kamfaci wannan hekta na noma, wani wata kuma sai na matsa gaba na debi wata hekta daya na noma.
“ Mu na amfani da takin dabbobi wajen yin noman kayan miyan da mu ke yi. Kada mutummya raina noma na don ya ji wai hekta daya kadai na ke nomawa a duk wata. Saboda wani zai iya shuka kayan miya 5000 a cikin hekta daya. Ni kuma har tsiro 26,000 na kan shuka a cikin hekta daya. Abin ya danganta ga albarkar da ake samu ta kayan miyan da mu ke shukawa.”
Yinka ta ce irin noman da ta ke yi na zamani ne, amma a gargajiyance ake yin noman.
“Kuma mu na yi wa manajojin gona horo, kamar yadda su ma masu gonaki mu na yi masu horon sanin makamar aikin gona da aikin noma na zamani. Mutane da dama na zuwa su na samun horo na tsawon watanni uku domin su fahimci yadda ake kasuwanci da harkokin noma.
“Mu a irin noman da mu ke yi ba mu amfani da takin zamani, sai dai takin gargajiya na dabbobi. Mu na samun kashin shanu da na wasu dabbobi.
“A gonar mu akwai ma’aikata biyar dukkan su ‘yan kasar waje da ke aiki a cikin ta. Sannan kuma akwai ma’aikata na wucin gadi da kuma yawan wadanda ke zuwa ana yi masu horon sanin makamar aikin noma. Kai har ta kai ga mun gina katafaren gidan kwana ma’aikata a cikin gonar mu.
“Na sha dibga asara a harkar noma. Amma wata rana sai na yi gamo-da-katar din wani littafi da kuma bidiyo na wata mata tare da mijin ta da ke noma hekta daya tal kuma ta na samun dala 100,000.
“Sai ni kuma na zauna na yi nazarin littafin kakaf, sannan kuma dama na kalli bidiyon na nakalce shi.” Inji Yinka, wadda ta ce daga nan ta kamo bakin zaren nasibin harkokin noma.”
“A shekara mukan bada horo ga manoma 50, wani lokaci har 100. Amma ya danganta ga yawan wadanda aka samu za a yi masu horon.
“Ina cajin naira 100,000 ga duk mutum daya. Kada ka ga kamar ina samun kudi da su. Amma su kuma su na samun fasaha da dabarun noman da na ke ba su labari da wadanda ake koya masu, wadanda in da a ce a wani wuri ne, sai sun kashe milyan daya kafin su samu basirar da su ke samu a hannu na.
“Wato kuma mu wani abin mamaki, ba mu amfani da injinan noma ko manyan motocin noma. Da kayan noma na gargajiya mu e amfani. Don idan ka yi amfani da injinan noma, to za su kashe mata kananan halittun da ke karkashin kasa, wadanda taki ne ga amfanin gonar kayan miyar da mu ke shukawa kuma mu ke raino.
“Batun kalubale kuma ai mu na fuskantar matsalar tsaro da barnar kayan gona da makiyaya ke mana.
“Za ka je gona kullum sai ka tarar da makiyaya sun banka shanun su a gonar ka. Yaya za ka yi? Ka yi magana ka janyo tashin hankali. Amma wasu mutanen su na yi wa gonaki ko lambunan su shinge. To ni a ina zan zan iya yi wa gona mai fadin hekta 12 shinge?”