Hausawa sun ce wai ‘ba a hada gudu da susar guiwa’. To amma ita wannan matashiyar mata ta hada gudu da susar guiwa har ma da murzar idanu, kuma a haka ta tsere wa miliyoyin mata fintinkau.
Hope Isaac, ba ta kammala karatun jama’a ba, a yanzu shekarar karshen kokarin samun digiri na daya ta ke, amma a cikin wannan yanayi ta mallaki gonakin noma, kiwon dabbobi da kuma kiwon zuwa a Jihar Imo.
Hope ta yi kasaitar da a yanzu ita ce Shugabar Kamfanin Hopifloral Resources. Kuma PREMIUM TIMES ta samu tattaunawa da ita, inda ta bada labarin lakanin da ta yi amfani da shi har ta samu nasibi a harkokin noma, kiwo da kuma kiwon zuma.
Duk da dai matar ta bada labarin irin gwagwarmayar da ta sha ita da makiyaya.
“Ka gan ni nan na fara zuwa gona tun cikin 2005, a lokacin ina bin mahaifiya ta, wadda masanar tattalin arzikin harkokin noma ce. To daga nan sai ta fara harkar noman rogo da kiwon kaji. Ni kuma na fara kiwon zuma cikin 2013.
“Na rika samun nasibin kara yawan gidan zumar da na ke kiwo daga amiya 10 zuwa 20 har 50. Sai kuma na fara noman rogo, samfurin da ake kira 419, kuma na fara kiwon kifi.
“Sai da makiyaya su ka bari gidajen zuma na sun yi yawa, sai su ka afka ciki, su ka ragargaza su, suka bar min kadan kawai. Duk da haka ban karaya. Na sayar dawasu na ci gaba da saka wasu.
“Shi kuma kiwon kifi, na fara ne a bayan gidan mu. Amma bayan watanni uku zuwa hudu, sai na samu kifaye masu nauyin kilogiram 700 zuwa 800, na kai na sayar.
“Sai kuma na tsunduma noman ‘kwakwamba’ a gona mai fadin hekta biyar. Na rika sayar wa malaman jami’a da dalibai.
“Ko cikin watan jiya sai da aka lalata min amiyar zuma har gida 30. Sai bayan kwanaki na sake kafa wasu gidan zumar. Amma ni ban taba yarda kalubalen da na ke fuskanta ya hana ni ci gaba da abin da na ke yi ba.
“Kai ni fa har tsutsotsi na ke kiwo, wadanda idan sun taru, na ke ciyar da kifayen da na ke kiwo da su.” Inji Hope.
Ta bayyana yadda ta samu horo a Shanghai Farms, kuma ta ce har yanzu ta na aiki da su.
“Kai ni fa ko zai daina kiwo, to ba za ni daina kiwon zuma ba. Ka ga a anzu lita daya ta kai naira 6,000. Ina sayar da zuma har ga likitoci. Kumai ta zuwa ba ta kwantai, jiran ta ake yi ka bedo a saye kawai.
“Abin da kuma na kara sa gaba a yanzu, shi ne bunkasa kiwon kaji, domin a yanzu dai wadanda na ke da su, ba su fi 400 ba ba.”
“Batun kalubale bai wuce matsalar isassun kudi ba, sai kuma makiyaya da ke lalata min gidajen zuma. Sau da yawa zuwa gonar ma dole ai na samu namiji ko maza sun raka ni, saboda matsalar tsaro. Wani lokaci sai ka ji ka samu makiyaya cikin gonar ka. Ka ga babu yadda za ka yi, sai dai ka bi su da lalama.
“Ina da masu yi min aiki kamar mutum hudu. Na kan kuma samu ‘yan ina-da-aiki kamar 17. Sai dai kuma a gaskiya mutane tsoron kudan zuma su ke yi. Amma ni na saba da su, tamkar abokai na ne, ba su yi min illa. Akwai kudan zumar da a cikin gidan ka ma za ka iya kiwon sa bai lahanta ka ba.” Inji Hope.
Hope ta bada labarin yadda ta rika sayen gonaki da kudaden cinikin zuma, inda a yanzu ta ce tsakanin gonakin da ta saya da kuma wadanda ta karba aro, ta kashe kusan naira milyan 8.
Ta ce sai da ta kai ta rika tara kudade a ‘microfinance bank’, inda bayannshekara daya, ta kwashi kudaden ta sayi gonaki da su.
Discussion about this post