HARKALLAR MAKAMAI: Kotun Daukaka Kara ta rushe tuhumar danne naira biliyan 2.1 da EFCC ke wa Dokpesi, Shugaban AIT

0

Kotun Daukaka Kara a Abuja, a ranar Alhamis ta fatattaki tuhumar danne naira biliyan 2.1 da ake yi wa Shugaban Kamfanin DAAR Communications Pls, mai gidan talbijin na AIT, Raymond Dokpesi.

An zargi Dokpesi, wanda kasurgumin dan PDP ne da laifin karbar naira biliyan 2.1 daga cikin kudaden da aka ware domin sayen makamai.

An tuhume shi da karbar kudaden daga hannun tsohon mashawarcin Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan kan tsaro, Sambo Dasuki, kafin zaben shugaban kasa na 2015.

Manyan Alkalai uku ne su ka zauna yanke hukuncin a ranar Alhamis, inda gaba dayan su su ka amince batun da Dokpesi ya tsaya a kai, cewa ba shi da wata tuhumar da zai amsa daga karar da Hukumar EFCC ta maka shi kotu.

Dokpesi ya ce tun farko Babbar Kotun Tarayya ce ta bayyana cewa akwai hujjar daga EFCC kan tuhumar da ta ke so a yi wa Dokpesi. Amma da bai gamsu ba, sai ya garzaya Babbar Kotun Daukaka Kara.

A zaman alkalai uku a ranar Alhamis, sun amince da cewa EFCC ta kasa gabatar wa kotu da hujjoji da shaidun da za su tabbatar da hutumar da ake wa Dokpesi, ballantana a yanke masa hukunci.

An dai zargi Dopkesi da kamfanin sa na DAAR Communications plc da laifin karbar naira biliyan 2.1 daga cikin kudin makamai, daga hannun Sambo Dasuki, kusa ga zaben 2015.

Lauyan Dokpesi da DAAR Communications, Kanu Igabi, ya roki Babbar Kotun Tarayya tun a shari’ar farko cewa a kori karar, domin dukkan shaidu 14 da EFCC ta gabatar, gurguwar hujja su ka gabatar.

Amma sai mai shari’a Dantsoho, wanda a yanzu shi ne Babban Mai Shari’a na Babbar Kotun Tarayya, ya yi watsi da rokon lauyan Dokpesi, tun a ranar 2 Ga Nuwamba, 2021.

Ganin haka sai babban lauya (SAN), Kanu Igabi ya daukaka kara a madadin Dokpesi da kamfanin sa, zuwa Kotun Daukaka Kara ta Tarayya.

Da ya ke karanto hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke a ranar Alhamis, Mai Shari’a Elfreda Williams-Dawodu, a madadin sauran alkalan biyu tara da shi kan sa, ya ce EFCC ta kasa gabatar da hujjoji gamsassu a kan Dokpesi da kamfanin sa.

Share.

game da Author