Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja Abuja (FCTA) ta bayyana kammala shirye-shiryen dawo da tsarin nan na ‘Park and Pay’, wanda ake karbar haraji daga duk wani mai motar da ya ajiye a fita ya shiga wani wuri, ko ya tsaya a wasu wurare da motar ta sa.
Mahukuntan Babban Birnin Tarayya sun bayyana cewa za a dawo da wannan tsari wanda aka rusa cikin 2014, domin a yanzu ana fuskantar yawaitar karya dokokin ajiye motoci ko tsayawa a wuraren da doka ta ce kada a tsaya ko kada a ajiye mota.
An dai daina wannan tsari na karbar kudi ne cikin 2014, bayan kotu ta bayyana cewa karbar kudade daga hannun masu ajiye motoci haramtacciyar hanya ce.
Sakataren Riko na FCTA Sashen Sufuri, Usman Yahaya ne ya sanar da dawo da wannan tsarin karbar kudade da ya bayyana wa manema labarai cewa za a fara aiki da shi tun daga ranar 1 Ga Mayu.
Yahaya ya bayyana cewa wannan tsari ya na cikin tarihin tsarin gina Abuja, domin an kirkiro shi ne don ya hana cinkoson motoci a kan titina.
Idan ba a manta ba, an maka FCDA kotu inda aka kalubalanci wannan dokar karbar kudade daga hannun wanda duk ya fita ya ajiye mota gefen titi ko kuma wasu kebantattun wurare.
A ranar 14 Ga Afrilu, 2014 kuma Babbar Kotun Abuja ta yanke hukuncin dakatar da karbar kudaden, bisa hujjar cewa ta haramtacciyar hanya a ke karbar kudaden.
Yahaya ya yarda cewa kafin a kotu ta haramta karbar kudaden a cikin 2014, jama’a da dama sun sha yin korafe-korafen cewa jami’an karbar kudaden na yi wa masu motoci wulakanci, ba su da da’a, rashin iya mu’amala da jama’a da kuma satar kudaden da su ke yi.
PREMIUM TIMES HAUSA ta tuna lokacin da aka rika kuka da jami’an karbar kudaden cewa, idan ka ba su manyan kudi, za su ce maka ba su da canji. Sai dai ka gaji da tsayuwa, ka bar masu sauran kudin ka, ka tafi ka na ‘Allah ya isa!’
Kamfanin Suntrust and Loans Ltd., ne ya maka FCTA kara kotu a wancan lokacin ya kalubalanci yadda ake tilasta wa masu motoci su na biyan haraji.
Mai Shari’a Peter Affen ne ya yanke hukuncin haramta karbar kudaden, bisa dalilin cewa a cikin dokar FCTA babu inda aka nuna cewa za a iya karbar haraji daga masu motocin da ke ajiyewa gefen titi.
A wancan lokacin an rika sa motocin janwe masu jan motoci sun a dauke motocin da aka ajiye bakin titi aka kai su wurin cin su tarar makudan kudaden haraji.
Amma a wannan karo, Yahaya ya ce kamfanonin da za su rika karbar kudaden kwararru ne, jami’an su ba za su rika zin zarafin masu motoci ba.
To amma da dama jama’a a Abuja a yanzu su na nuna damuwa dangane da yadda ake ajiye motoci barkatai a gefen titi.
“Yanzu fa a Abuja ta kai har za ka rika ganin dillalan motoci na ajiye motocin sayarwa a gefen titi, daidai layin da motocin haya ke tsayawa su na daukar fasinja. Wasu ma a kan titin da masu tafiya a kasa ke bi sun a wucew. A nan su ke ajiye motocin su, domin mai sha’awar saye ya gani a yi ciniki. Inji Alhaji Ibrahim, wanda ke yawan nuna damuwar sa idan ya rasa wurin da zai ajiye motar sa a wajen bankin Access Bank na Garki, Abuja.
Ya yi wannan korafin ne wata rana da ya gano cewa yawancin motocin da ake ajiyewa gefen titi kusa da bankin, duk na sayarwa ne, ba na masu shiga cikin bankin ba ne.