Har asarar makudan daloli mu ke yi don dai mu rika sayar da siminti a Najeriya –Dangote

0

Kamfanin Simintin Dangote, Dangote Cement Plc, ya karyata zargin tsawwala farashin siminti da ake cewa ya na yi a cikin Najeriya, fiye da sauran kasashe.

Maimakon haka, kamfanin ya bayana cewa har asarar makudan daloli ya ke yi cikin Najeriya, don dai kawai ya rika sayar da simintina cikin kasar nan.

Kamfanin ya bayyana cewa farashin naira 2,450 ake sayar da buhun siminti daya daga masana’antar Obajana, sannan masana’antar Gboko daga can ana sayarwa naira 2,510 ne.

Babban Daraktan kamfanin mai suna Devakumar Edwin, shi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Lokoja, a ranar Talata.

Ya kara da cewa farashin wanda ya bayyana a sama, shi ne farashin kowane buhun siminti har zuwa ranar Talata, 12 Ga Afrilu, kuma a ciki har da kudin harajin jiki magayi, wato VAT.

Ya kara da cewa fitowa yin wannan karin haske ya zama wajibi, saboda rahotannin da ake ta samu cewa Dangote na sayar da buhun siminti a Najeriya da tsada, fiye da yadda ya ke sayarwa a kasashen irin su Ghana da Zambia.

“Yayin da ake sayar da buhun siminti kusan dala 5.1, cikin kudin kuma har da harajin VAT da za a rika cire wa Najeriya, to a Ghana buhun siminti ya na kamawa dala 7.2, sai a kasar Zambia kuma buhu daya na kamawa dala 5.95.” Inji Edwin.

Ya kara da cewa duk da kamfanin ya na da karfin kayyade farashi daga masana’anta, to amma idan kaya sun shiga hannun ‘yan kasuwa babu yadda kamfanin Dangote zai iya tirsasa masu sari su rage farashi, domin ya rigaya ya fita daga hannun kamfani.

Edwin ya nuna bacin rai tare da yin kira a guji yada ji-ta-ji-ta da labarai na karairayi, masu nuna cewa Dangote na sayar da siminti da tsada a Najeriya, fiye da sauran kasashen Afrika.

Sai ya danganta tsadar siminti da ake samu a kasuwanni na da nasaba da barkewar cutar korona da ta addabi kasashe daban-daban. Ya ce bukatar siminti ta haddasa tsadar sa a hannun ‘yan kasuwa, ba Dangote ba ne ya kara farashi daga kamfani.”

Y ce a bangaren su, tsarin hada-hadar kudaden kasar waje duk iri daya ne. an samu karin farashin kayan aiki a masana’antun siminti.

“Sai da ta kai mun dakatar da fitar da siminti zuwa kasashen waje daga Najeriya, don dai mu wadatar da shi a nan cikin kasa, saboda bukatar sa da ake da ita sosai.

“To wanda ya ki fitar da kayan sa don sayarwa waje, ai ya yi asarar makudan daloli.” Inji shi.

Ya ce tun 2019 rabon da kamfanin Dangote ya kara farashin siminti, duk kuwa da cewa kashi 50 bisa 100 na hada-hadar ayyukan kamanin, duk da daloli a ke cinikayyar su tsakanin kamfanin.

Share.

game da Author