Gwamnatin Najeriya ta kara wa’adin wata daya domin kowa ya samu damar hada katin dan kasa da lamba ko lambobin wayoyin sa na GSM.
Cikin wata sanarwa ta nuna cewa Gwamnatin Tarayya ta ce zuwa yanzu sama da mutum milyan 51 ne su ka samu nasarar yin rajistar katin dan kasa (NIN), wanda a yanzu tilas sai da lambar katin shaidar ce za a iya yi wa duk wani dan Najeriya rajistar samun wasu damammaki, ciki kuwa har da samun katin fita kasashen waje da kuma lasisin tukun mota.
Sanarwar ta fito ne a cikinn wata sanarwar hadin guiwa wadda Hukumar Sadarwa ta Kasa da Hukumar Samar da Katin Dan Kasa su ka sa wa hannu tare.
Sun kuma bayyana cewa gwamnati ta kara wa’adin hada layin wayoyi da katin dan kasa daga nan zuwa ranar 6 Ga Mayu, 2021.
“An gabatar da bukatar neman karin wa’adin ga Shugaba Muhammadu Buhari, inda shi kuma nan take ya amince da yin karin wa’adin na wata daya tal.”
Bukatar karin ta taso ne a wurin taron kwamitin hada lambobin waya da lambar katin shaidar dan kasa, wanda Ministan Sadarwa Ali Pantami ke shugabanci.
Wasu da su ka halarci taron sun hada da wakilan kamfanonin wayoyin sadarwa da su ka hada MTN, Glo, 9Mobile da Airtel da sauran su.
Shugaban Kwamiti, Minista Isa Pantami ya ce hada lambar katin waya da lambar katin shaidar dan kasa ai taimaka wa gwamnati da jami’an tsaro wajen sauri da saukin gano masu aikata laifuka daban-daban.s