Gwamnonin Kudu-maso-gabas sun fito da sabbin matakan samar da tsaro bakwai

0

Gwamnonin jihohin Kudu-maso-gabas sun gudanar da taro a Enugu domin tattauna matakan gaggawa na magance matsalar tsaron da ta darkaki yankin har ta zama kamar wutar-daji.

Wannan taro da su ka yi dai shi ne taron su na gaggawa na biyu a cikin makonni biyu.

An yi taron ranar Lahadi a Enugu kwana biyu bayan mahara sun kai wa gidan Gwamna Hope Uzodinma da ke kauyen su hari da bidigogin roka.

Gwamnonin Enugu, Ebonyi, Abia, Anambra da Mataimakin Gwamnan Imo duk sun halarci taron.

Haka Karamin Ministan Tama da Karafa, Okechukwu Ogah ya halarta, shi da Shugaban Kungiyar Kabilar Igbo Zalla ta Ohanaeze Ndigbo, Shugaban CAN na Shiyyar Kudu-maso -gabas, Sarakunan Gargajiya da manyan jami’an tsaron da ke kula da shiyyar duk sun halarta.

Kudirori Bakwai Da Gwamnonin Kabilar Igbo Za Su Maida Doka:

1. An umarci Kwamishinonin Shari’a na jihohin kabilar Igbo biyar su zauna su fito da daftarin da zai bayar da ikon kafa Jami’an Tsaron Hadin Guiwa a Jihohin Kudu-maso-Gabas.

2. Za a kafa Hukumar Bada Shawarwarin Tsaro ga Jami’an Tsaron Hadin Guiwa da za a kafa nan ba da dadewa ba.

3. An haramta kiwo sakaka cikin dazukan jihohin Enugu, Ebonyi, Imo, Anambra da Abia.

4. Gwamnonin biyar sun kara jaddada goyon bayan su kan lallai a sake fasalin Najeriya, wato ‘restructuring’.

5. Gwamnonin biyar sun jaddada cewa lallai a bada iko ga kowace jiha a Najeriya ta kafa ‘yan sandan jiha na ta na kan ta.

6. Gwamnonin sun kudiri aniyar gaggauta fito da tsare-tsaren Inganta Rayuwar Matasa, wanda tun bayan tunzirin #EndSARS aka nemi a kirkiro domin rage yawan zauna-gari-banza masu tayar da fitintinu.

7. An nada Shugaban Kungiyar Kabilar Igbo Zalla, Ohanaeze Ndigbo ya zama Shugaban Kwamitin Samar da Zaman Lafiya da Sasanta Rashin Jituwa a Kudu-maso-Gabas.

Share.

game da Author