Gwamna Bala na Bauchi ya raba motocin aiki 50 ga hukumomin tsaron jihar

0

Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad a ranar Asabar ya kaddamar da rabon matocin aiki wa hukumomin tsaro na jihar.

Babban mai ba gwamna Bala shawara kan harkokin Yada labarai, Mukhtar Gidado wanda shine ya fitar da wannan shela, ya bace an gudanar da bikin mika motocinbga rundunonin tsaro a jihar ranar Asabar.

A lokacin da yake kaddamar da rabon motocin wadda ya gudana a gidan Gwamnatin jihar Bauchi, gwamnan yace duka motocin aikin akwai na’urar Sadawrwa na zamani a cikinsu domin samar da saukin wajen samun bayanai a tsaknin jami’an tsaron.

Sannan kuma ya kara da cewa samar da wadannan motocin nada daga cikin tsarin gwamnatinsa da maida hankali wajen ganin an dakile matsalolin tsaro da addabi mutane da ya hada da yin garkuwa da mutane satar Shanu fashi da makamirikice rikice da dai sauran su.

Gwamnan wadda yace tsaron lafiya da dukiyoyin al’ummah sune gwamnatin ta maida hankali akai ya ce wadannan kayan aiki za su taimaka wajen kau da ire-iren wadannan razhin tsaro da ake fama da su.

A nasa jawabin IGP Usman Alkali, wanda ya samu wakilcin AIG Mr. Johnson Babatunde Kokumo, yace
“Maigirma gwamna, Muna godiya da irin hubbasan da ka yi na samar da motocin aiki, Zamu Kuma yi aiki dasu yadda ya kamata.

Share.

game da Author