A wani kazamin rikici tsakanin kabilun Lunguda da na Waja, akalla an tabbatar da mutuwar mutum 15 a wani kazamin rikicin kabillanci da ya barke ranar Litinin da dare, a kauyukan Nyuwar da Jessu, cikin Karamar Hukumar Balanga ta Jihar Gombe.
Gwamna Inuwa Yahaya ne ya bayyana haka a ranar Talata, yayin da ya ke magana da manema labarai, jim kadan bayan duba irin barnar da mummnunan fadan ya haddasa.
Kashe-kashen dai ya faru ne tsakanin kabilun Lunguda da Waja wadanda ke zaune kusa da juna a yankunan jihar Gombe.
Gwamna Yahaya ya nuna tsananin mamakin irin mummunar barnar dukiyoyi da rasa rayukan da aka yi.
“An shaida min a garin Nyuwar an kashe mutum takwas. Nan kuma a kauyen Hemen cikin al’umma Jessu an kashe mutum bakwai. Kun ga mutum 15 kenan. To a gaskiya ba za mu yarda da irin wannan ba.”
Gwamnan ya bayyana cewa ya kakaba dokar hana fita da walwala a yankin, domin a bai wa jami’an tsaro damar dawo da doka da oda a yankunan da aka yi tashin hankalin.
Ya kara da cewa dukkan wadanda su ke da hannu sai sun dandana kudar laifin da su ka aikata, domin sai an kamo su, kuma sai doka ta hau kan su da hukunci mai tsanani, daidai da abin da su ka aikata.
Sannan kuma ya umarci Kwamishinan ’Yan Sanda na Gombe, Ishola Babaita da sauran jami’an tsaro su tabbatar cewa irin haka ba ta sake faruwa a wadannan kauyuka da jihar Gombe ba.
Ya kuma shaida wa wadanda lamarin ya shafa cewa gwamnati za ta tura masu kayan agaji da abinci ba da dadewa ba.
Yayin da Kwamishinan ‘yan Sanda ya shaida wa Gwamna Yahaya cewa ya tura isassun jami’an sa a yankin kauyukan da aka yi kashe-kashen, shi kuma Wakilin Nyuwar, Yohanna Gaimaka, ya bayyana wa Gwamna cewa mutanen kauyen sa na sun yi gudun hijira sun tsere zuwa wasu wurare.
Gaimaka wanda ya barke da kuka a lokacin da ya ke yi wa gwamna bayani, ya ce mutanen Waja ne su ka fara kai masu hari.
Shugaban na kabilar Lunguda ya ce an fara kai masu hari ne tun a ranar Litinin wajen karfe 9 na dare, har wayewar gari a ranar Talata.
“Mu kabilun Lunguda da kabilun Waja mun dade tsawon shekaru mu na zaune da juna lafiya a nan cikin Jihar Gombe. Amma abin da ya faru jiya, bala’i ne mai firgitarwa.”
Discussion about this post