Magoya bayan jam’iyyar PDP sun ba hammata iska a wurin zaben shugabannin Jam’iyyar na yankin Arewa Maso Yamma da aka yi a Kaduna ranar Asabar.
Rahotanni sun bayyana cewa magoya bayan jiga-jigan Jam’iyyar biyu, Rabiu Kwankwaso da na Gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal sun kaure da fada bayan sun ki amincewa da juna kan ‘yan takarar da aka tsayar su shugabanci jam’iyyar a shiyyar.
Kwankwaso na zargin gwamnan Jihar Sokoto Aminu Tambuwal da yi wa jam’iyyar katsalandan a ayyukan ta a Kano.
An zo wurin zabe tiryan tiryan sai fada ya kaure, aka bi akwatinan aka farfasa, sannan aka kekketa takardun zaben, taro ta tarwatse.
Yanzu dai ba a san halin da ake ciki ba sai an saurari jawabi daga uwar jam’iyyar don sanin ina aka dosa.