Wasu masu ikirarin bin jihohi da kananan hukumomi 774 bashin naira biliyan 159, sun kama aikin bata sunan Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi, saboda ya hana a biya kudaden, sai an tabbatar da hujjar cewa su na bin basussukan tukunna.
Cikin makon da ya gabata ne PREMIUM TIMES ta fallasa gidogar zargin gaggawar da rawar jikin da su Ministan Shari’a Abubakar Malami su ka rika yi, domin su biya bashin da Hukumar EFCC, Kungiyar Gwamnonin Najeriya da Kungiyar Shugabannin Kananan Hukumomi su ka yi gargadin cewa kada a biya bashin, har sai an tabbatar da hujjoji masu gamsarwa tukunna.
Mun kuma buga labarin yadda aka yi kokarin bata wa Gwamna Fayemi suna aka ce ya ki amincewa a biya kudaden saboda ya nemi wani kaso daga kudaden idan an biya, amma an hana shi.
Bayan PREMIUM TIMES ta buga labarin da Fayemi ya bayyana cewa an nemi a ba shi cin hancin dala milyan 80 idan ya amince a biya su kudaden da su ka ce su na bi bashi.
Buga labarin ke da wuya sai daya daga cikin masu ikirarin bin bashin mai suna George Uboh ya yaye hijabin da ke fuskar sa, ya fito fili ya ce tabbas Fayemi ya nemi a ba shi cin hanci ta hannun wasu jakadun sa kuma na hannun damar sa mutum biyu.
“Gwamna Fayemi ya na dabara ce kawai ya na rubuta wa Shugaban Kasa da Ministar Kudade wai kada a biya mu kudaden mu. Alhali kuma a bayan fage ya na turo mana wasu aminan sa biyu ana tattauna cin rashawar da za a ba shi daga cikin kudaden.”
Hada dai Udoh ya yi wannan kakkausan ikirari. Shi ne Shugaban Kamfanin Panic Alert Security System (PASS) Limited.
Ya kara da cewa “Gwamna Fayemi na da maitar neman zama shugaban kasa a zaben 2023 ido-rufe. Kuma yaudara ce ya ke yi da har ya ke nuna a sarari kamar ya fi kowa gaskiya a fadin kaar nan.”
“Gwamna Fayemi ka daina borin-kunya. Mu na da hujjojin yadda ka turo aminan ka biyu domin su nemar maka kashi 10 bisa 100 na kudaden. Amma ni George Udoh ba zan ba ka ko kwandala daga kudaden da ba ka yi gumi ka samu ba.”
PREMIUM TIMES ta binciko cewa an taba daure Udoh a Amurka saboda samun sa da laifin harkallar katin cirar kudi na banki. A nan Najeriya ma an taba yanke masa hukunci a kan laifin cin amanar da ta jibinci Hrkokin kudade.
Ya kuma kaluballanci Gwamna Fayemi ya fito da sunayen mutanen da ya ce sun iske hi har cikin ofis su ka yi masa tayin dala 80,000 idn ya amince aka biya su kudaden.
PREMIUM TIMES dai ta buga labarin yadda ikirarin da Gwamna Fayeni ya yi, inda ya ce ’yan gidoga su ka nemi ba ni cin hancin dala miliyan 80 don na yi shiru.
Fayemi Fayemi ya shaida cewa wasu ’yan kakuduba aka turo musamman su ka ce za a ba shi dala milian 80 idan ya amince aka biya su kudaden.
Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti, kuma Shsugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, ya bayyana a ranar Litinin cewa wasu ’yan gidoga sun same shi gaba da gaba, su ka yi masa alkawarin cewa idan ya amince aka biya bashin da kotu tace a biya su na dala miliyan 418, to za su ba shi cin hanci har na naira bliyan 80.
Bashin dai wanda ake tankiya a kai, masu neman a biya su bashin sun yi ikirarin cewa jihohi da kananan hukumomi ne ake bi bashin a daidai lokacin da ake kkarin karbo kudade da ga Paris Club.
Sun ce sun yi wa jihohi da kananan hukumomin kasar nan 744 ayyuka ne bashi, bisa yarjejeniyar cewa idan aka biya jihohi da kananan hukumomi kudaden Paris Club, to za su biya su.
A cikin wata tattaunawa ta musamman da Gwamna Fayemi ya yi da PREMIUM TMES, ya bayyana cewa da farko alkawarin ba shi dala miliyan 40 su ka yi. Ya ce ba ya bukata, kuma ba zai bari a biya su kudaden ba, tunda babu wata hujjar da ke nuna cewa sun yi ayyukan da su ke ikirarin sun yi.
Fayemi ya ce sun sake samun sa, su ka yi masa alkawarin biyan sa toshiyar baki ta dala miliyan 80, wato nunkin dala milyan 40 kenan. A nan ma gwamnan ya ce ba ya bukata, ba zai karba ba.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda kakudubar ta ke da kuma yadda Ministan Shari’a Abubakar Malami, Ministar Harkokin Kudade Zainab Ahmed da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Ibrahim Gambari su ka rika kokarin su ga an biya ‘yan kakuduba kudaden, duk kuwa da cewa Kungiyar Gwamnanonin Najeriya sun kai wa Shugaba muhammadu Buhari takardar cewa kada biya kudaden, har sai an yi kwakkwaran binciken kwakwaf an tabbatar tukunna.
Baya ga gwamnnin, Hukumar EFCC da Kungiyar ALGON ta shugabannin kananan hukumomin Najeriya, ita ma ta yi kashedin kada a biya kudaden, duk ga Minista Malami, amma ministan ya kauda kai daga gargadin su, ya ci gaba da kokarin ganin sai an biya kudaden daga kudaden jhohi da kananan hukumomi.
“Wato maganar gaskiya mamaki ya kama ni ganin yadda wadanda aka turo mn ko kunya ba su ji ba, su ka tunkare ni da batun ba ni cin hanci har na dala milyan 40. Daga nan su ka nunka farashi zuwa dala milian 80.” Inji Fayemi.
Fayemi a ce shi bai kullaci wadanda su ka yi ikirarin su na bin bashin ba. Kuma bai ce ba ya so a biya su ba, amma abin da ya jajirce a kai a matsayin sa na Shugaban Kungiyar Gwamnnin Najeriya, shi ne kafin a bia kudaden, a fara gudanar da binciken kwakwaf domin a gano shin sun yi ayyukan ko kuwa ba su yi ba.
Ya kara da cewa maganar neman a biya shi cin hanci na dala har miliyan 80, hakan na kara tabbatar da cewa akwai lauje a cikin nadi.