Gidauniyar Adamu Gwarzo ta baiwa KadPoly kyautar dankareriyar motar daukar dalibai

0

A ci gaba da tallafawa wa manyan makarantun Najeriya da gidauniyar Adamu Abubakar Gwarzo ya ke yi, a karshen makin jiya ya yi wa Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kadyna, KadPoly kyautar babban mota daukan dalibai.

Wannan kyau ta daya ne daga cikin kyaututtukan da gidauniyar ke yi wa jami’o’in Kasar nan.

A cikin watan Faburairu, gidauniyar karkashin shugabancin Farfesa Adamu Gwarzo, ya mika wa jami’ar Bayero, BUK dake Kano kyautar irin wadanan motoci har guda biyar.

Haka kuma ya baiwa jami’ar Umaru Musa irin wannan bas din.

Farfesa Adamu Gwarzo ne shugaban jami’ar Maryam Abacha da ke Nijar da kuma wanda aka kafa a Najeriya, a jihar Kano.

A jihar Kaduna ma, Farfesa Adamu Gwarzo ya kafa sabuwar jami’a mai zaman kanta wanda take gab da aka kaddamar da ita.

Share.

game da Author