Kwamitin Majalisar Tarayya da aka kafa domin ya binciki ikirarin da Mashawarcin Shugaba Muhammadu Buhati a Fannin Tsaro, Babagana Monguno ya yi cewa makudan kudaden da aka ware domin a sayo makamai a karkashin su Janar Mai Ritaya Tukar Buratai sun bace, kuma ba a sayo ko barkonon tsohuwa ba, ya gayyaci sabon Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Janar Ibarahim Attahiru.
A ranar Litinin ce Attahiru ya bayyana a gaban kwamitin binciken, bayan a baya ya kasa bayyana a gayyatar farko da su ka fara yi masa har sau uku.
A ranar 22 Ga Maris ne dai aka gayyaci Attahiru wanda ba a lokacin sa aka salwantar da dala bilyan daya da Monguno ya yi zargi ba, aka gayyaci Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefile, amma duk ba su bayyana ba.
Haka ma a ranar 7 Ga Afrilu, an nemi su bayyana, amma ba su bayyana din ba.
Sai dai kuma a bayyanar da ya yi a ranar Litinin, Attahiru ya bayyana wa kwamitin bincike cewa ya kasa bayyana ne saboda wasu muhimman sha’anonin da su ka sha kan sa, wadanda kuma duk sun jibinci matsalolin tsaron kasar nan.
Sai dai kuma bai bada hakuri ba, inda ya ce bayanin da ya yi masu ya wadatar.
TSAKANIN BIRBIRI (PDP) DA JEMAGE (APC): Dalla-Dallar Zargin Harkallar Kudaden Makamai: Gwamnatin Buhari ta shafe shekaru ta na binciken tsoffin jami’an gwamnatin Buhari bisa zargin harkallar cin biliyoyin dalolin kudaden makamai.
Sai dai kuma shekaru biyar bayan kakkabe PDP kan mulki, ita ma gwamnatin Buhari ta shiga cikin wannan zargin, wanda ya fara fitowa daga Mashawarcin Shugaba Buhari kan Harkokin Tsaro, Babagana Monguno.
Tuni dai Majalisar Tarayya ta kafa Kwamitin Binciken wadanda su ka yi wa biliyoyin dalolin kudaden makamai luguden wuta.
‘Hakallar Makamai: ‘Ba A Tambayar Kaza Hanyar Rafi, Sai Agwagwa’ -Attahiru
Janar Attahiru ya bayyana cewa ba zai ce komai ba dangane da batutuwan da aka nemi ya yi bayani a kai, wadanda su ka shafi salwantar dala bilyan 1 da aka yi zargi.
Shi dai Attahiru ya kama aiki ne bayan an fitar da kudaden, kuma da ya hau kan mukamin ne aka ce ya duba bai ga kudaden ba, kuma babu makaman da aka ware kudaden domin a sayo makaman yaki da Boko Haram da ‘yan bindiga.
“Wannan babbar magana sai dai a tambayi wadanda ke da ruwa da tsaki a kan batutuwan a cikin hukumar sojoji.”
Attahiru ya yi wannan furucin ne yayin da Honarabul Bede Eke ya ce idan zai yi bayani, to ya fara da rantsuwar-kaffarar-kwansitushin tukunna.
A kan haka shi kuma sai Shugaban Kwamitin Bincike Honorabul Olaide Akinremi, ya yi kokarin hana kai ruwa rana, ko kuma tayar da jijiyoyin wuya, inda ya ce to shikenan, akwai bukatar yin wannan magana a gaban zaman zauren majalisa na musamman.
AN KI CIN BIRI AN CI KARE: Yadda Aka Yi Wa Kudin Makamai Luguden Wuta A Zamanin Su Buratai – Monguno, Mashawarcin Buhari
“ Wannan gaskiya ce tabbas cewa an ware bilyoyin nairori domin sayen kayan makamai a zamanin wannan gwamnatin, amma wadanda aka damka wa alhakin kudaden sun ragargaje su, an nema ko sama ko kasa, an rasa inda kudin su ke.”
Mashawarcin Buhari a Harkokin Tsaro, Babagana Monguno, ya fallasa cewa an ware wasu kudade a karkashin wannan gwamnatin domin sayen makamai a karkashin Manyan Hafsoshin Tsaron da su ka sauka kwanan nan, amma an ragargaje kudin, ko albarushi ba a sawo da kudaden ba.
Haka da Mashawarcin kan Harkokin Tsaro, kuma Manjo Janar Mai Ritaya Babagana Monguno ya bayyana, a wata tattaunawa da ya yi da BBC a ranar Juma’a.
Babagana ya fallasa wannan satar kudade wata daya bayan Buhari ya sauke manyan hafsoshin tsaron, cikin su har da Tukur Buratai.
Makonni biyu bayan sauke su, sau kuma Buhari ya sake yi masu wata sakayyar da aikin jakadanci zuwa wasu kasashen da har zuwa yau dai ba a bayyana kasashen da aka tura kowanen su ba.
A wannan fallasa mai ban-mamaki, Monguno ya ce yayin da wadannan sabbin manyan hafsoshi su ka kama aiki, sun nemi makaman da su ka kamata a sawo da makudan kudaden, amma ko albarushi babu.
Haka nan kuma sun nemi inda aka ajiye makudan kudaden, nan ma ko karfanfana ba su samu ba.
Yayin da ya kara da cewa ba sata ya kala wa su Buratai ba, to amma dai an nemi kudaden babu, kuma babu makaman da ya kamata a ce sun sawo da kudaden.
“Yanzu dai sabbin Manyan Hafsoshin Tsaro sun kama aiki. Amma kuma sun rasa inda kudaden da aka ware wa tsoffin hafsoshin da aka cire su ke, domin dai ba a sawo makaman da kudaden ba.” Inji Monguno
“Ina tabbatar maku cewa Shugaban Kasa lallai zai binciki inda kudaden su ke. Su ma Gwamnonin Najeriya su na mamakin yadda aka yi da kudaden. Amma ina tabbatar maku Shugaban Kasa zai sa a yi bincike.”
“Yanzu dai binciken farko ya tabbatar da cewa babu kudin, kuma babu makaman da aka ware kudin domin su.”
PDP Ta Nemi Gwamnatin Buhari Ta Fito Da Dala Bilyan 3.5 Na Kudaden Makamai Da Aka Yi Zargin Sun Salwanta:
Kwanan baya sai da PDP ta nemi Gwamnatin Buhari ta yi wa ‘yan Najeriya bayanin yadda kudin makamai dala bilyan 3.5 su ka salwanta.
Jam’iyyar PDP ta kaluballanci Gwamnatin Shugaba Muhammmadu Buhari cewa ta gaggauta fitowa ta yi wa ’yan Najeriya bayanin yadda dal bilyan 3.5 da aka ware domin sayen makamai su ka salwanta, tunda ba a sayo makaman ba.
Haka kuma PDP ta yi kira ga Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya su gaggauta binciken kwakwaf domin gano gaskiyar yadda aka karkatar da kudaden, da kuma wadanda su ka karkatar da su.
PDP ta yi wannan kakkausan kalubale ga gwamnati da kuma kira ga majalisu ne a cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na jam’iyyar, Kola Ologbondiyan ya fitar ga manema labarai a ranar Alhamis.
Jam’iyyar adawar ta ce sabuwar harkallar cuwa-cuwar dala bilyan 2.5 da ake zargin Mashawarcin Buhari kan Harkokin Tsaro, Babagana Monguno na da hannu, wanda shi ma a kwanan baya ya zargi su Buratai sun yi sama-da-fadin dala bilyan 1, sun bayyana cewa babu abin da ke wakana a karkashin gwamnatin Buhari sai masifar jidar makudan kudade.
“Ya kamata Majalisa ta gaggauta gudanar da kwakkwaran binciken gano inda aka karkatar da wadannan makudan kudaden da ya kamata a ce an sayo makamai da su domin a kare rayukan jama’a. Maimakon haka sai zargin karkatar da kudaden ke ta fitowa a karkashin gwamnatin Buhari.
“Irin yadda bangaren tsaron gwamnatin Buhari ke fallasa junan su dangane da zargin karkatar da kudaden makamai, ya nuna yadda ake tseren wuce juna tsakanin manyan jami’an gwamnatin Buhari, su na takarar wanda ya fi wani azurta kan sa da kudaden talakawan da su ka kamata a sayo makamai a kare rayukan su da dukiyoyin su.”
PDP ta ragargaji APC ta da cewa maimakon jam’iyyar ta goyi bayan talakawan kasar nan, sai ta buge da borin-kunyar kokarin kare jami’an gwamnatin da ake zargi sun yi wa junan su watandar kudaden.
Ban Yi Wa Makuden Kudaden Makamai Luguden Wuta Ba –Buratai:
Tsohon Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Tukur Buratai ya bayyana cewa babu ruwan sa da harkallar Dala Biliyan daya da aka fidda don sayen makamai.
A wata takarda wadda lauyan sa, Osuagwu Ugochukwu, ya sa wa hannu, Buratai ya ce a iya sanin sa bai san da wata dala biliyan 1 da aka taba ba shi wai na makamai kuma tsoffin manyan hafsoshin Najeriya su ka yi awon gaba da su ba.
“ Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Mungono wanda aka danganta wannan kalamai da shi ya ce ba haka ya fadi ba. Saboda haka muna kira ga mutane su daina cewa wai su Buratai sun waske da kudin makamai.”
A karshe lauyan ya gargadi masu ci gaba da yayata wannan magana da babu gaskiya a cikin ta cewe kotu ce za ta raba su.
A yau Talata ce kuma Kwamitin Binciken Salwantar Kudaden Makamai ya gayyaci Sufeton ‘Yan Sanda Kasa, dangane da da wannan badakala.
A baya jami’an gwamnatin PDP ce aka tasa a gaba. Yanzu kuma tun APC ba ta kammala wa’adin ta ba, ana neman tsayar mata da alkiyamar ta kafin saukar ta daga mulki.