Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da sanarwar gaggauta rufe Kwalejin Fasaha ta Bagauda, wato Bagauda Technical Collage, a ranar Litinin.
Rufe kwalejin a gaggauce ya biyo bayan wani rahoton barazanar matsalar tsaro da aka gabatar wa gwamnatin jihar.
Kwalejin wadda ke cikin Karamar Hukumar Bebeji, ta na kan hanyar Kano zuwa Jos.
Cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Ilmi ta Jihar Kano, Aliyu Yusuf, ya raba wa manema labarai ranar Litinin a Kano, ya ce Kwamishinan Ilmi Sanusi Kiru ne ya yi sanarwar rufe kwalejin da kan sa.
“Mun samu rahoton barazanar rashin tsaro mai tayar da hankali dangane da kwalejin. Don haka mu ka gaggauta rufe ta, domin kare rayukan dalibai da malaman kwalejin.
“Ana sanar da iyayen yara kowa ya gaggauta zuwa kwalejin ya dauko dan sa da ke karatu a can.” Inji sanarwar.
An dade tun farkon wannan shekara makarantun sakandare na kwana a Arewa ke zaman dar-dar biyo bayan yawan kai farmakin kwasar su ana yin garkuwa da su da ‘yan bindiga ke yi.
An kwashi dalibai a jihohin Katsina, Zamfara, Neja da Kaduna.