GANDUJE: Zargin karbar cin hancin Daloli: ‘Yan sanda na farautar Ja’afar Ja’afar

0

Mawallafin Jaridar Daily Nigerian Ja’afar Ja’afar ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya na neman sa ruwa a jallo ne saboda ya bidiyon da ya wallafa na karbar cin hanci daloli da aka nuna gwamnan Kano Abdullahi Ganduje na karɓa.

A wata wasika da rundunar ‘yan sandan kasa ta rubuta wa Ja’afar, ta hannu A.A Elleman, dake ofishin Sufeto Janar din Najeriya, rundunar na bukatar Ja’afar ya bayyana a hedikwatar rundunar ƴan sanda ta kasa, a Abuja domin yin bayani game da wasu korafe-korafe da aka shigar a kan sa.

Waɗannan ƙorafe-ƙorafe kuwa sun haɗa da, ɓata suna, yin zagon ƙasa, shirga ƙarya da neman ingiza mutane su tada husuma da keta wa ofishin sufeto janar din ƴan sandan Najeriya rigar rashin mutunci wanda aka samu yana da hannu a ciki.

” A dalilin haka rundunar ta ke bukatar mawallafin jaridar ya bayyana a ofishinta domin amsa wasu tambayoyi akan waɗannan Zargi.

Sai dai kuma tuni , Ja’afar ya yi layar zana, inda ya shaida cewa dole yayi haka domin kansa da iyalan sa.

” Babu abinda ya haɗani da sufeto janar din ƴan sandan Najeriya, ban taɓa wani rubutu akan sa ba na ɓatanci ko tun a baya ma. Rufa-rufa kawai ake yi min, idan na bayyana hedikwatar ƴan sandan sai su damke ni.

Idan ba a manta ba jaridar Daily Nigerian ce ta fara wallafa wasu bidiyo da ke nuna gwamnan Kano Abdullahi Ganduje na karkacewa ya na cusa bandir din daloli a aljufan kaftanin sa.

Ana zargi wadannan kuɗaɗe da gwamna Ganduje ke karɓar su daga hannun wani dan kwangila ne da ya ke mika masa kason sa na cin hancin wata kwangila da gwamnatin jihar ta ba su.

Share.

game da Author