Femi Adesina ya shirga karya ne yanko yawan adadin wadanda basu da aiki yi Najeriya da yayi a 2015 – Binciken Dubawa

0

Mai baiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, shawara kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya kantara karyar yawan mutane marasa aikin yi ne a 2015.

Zargi: Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai ya taba fadin cewa wai yan Najeriya akalla miliyan 30 ne basu da aikin yi a Najeriya a lokacin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta fara aiki a zangon ta na farko, wato 2015.

Adesina ya furta wadannan kalamai ne yayin da yake hira da gidan talbijin din Channels, a shirinsu na siyasa wato Sunday Politics ranar 28 ga watan Maris 2021.

Tantancewa

Mun fara tantance wannan labarin ne da sauraron hirar ta Adesina da Seun Okinbaloye jagoran shirin na Sunday Politics mai tsawon minti 52 da sakan 42 wanda aka sanya a shafin tashar a Youtube.

Adesina ya yi bayanin cewa a shekarar 2015 jam’iyyar APC ta gano cewa mutum miliyan 30 ne adadin wadanda basu da aikin yi a kasar nan.

Adeshina ya fadi hakan ne yayin da ya ke amsa tambaya dangane da yawan marasa aikin yi a kasar bayan alkawarin gwamnatin na samar da aikin yi ga ‘yan kasa.

“Kafin zaben 2015 lokacin da jam’iyyar APC ke yakin neman zabe, alkaluman da Buhari ya gani kuma ya ke amfani da su sun nuna cewa akalla mutane miliyan 30 ba su da aikin yi musamman matasa kuma wannan gawamnatin za ta yi wani abu akai. Tsakanin shekarun 2014/2015 miliyan 30 ne aka tantance a matsayin marasa aikin yi. Yana nan a rubuce” In ji Adesina

Dubawa ta fara da binciken kalmomin da suka danganci matsayin rashin aikin yi a shekara ta 2015. Wannan ya kai mu ga rahotanni kamar haka:

Wani rahoto daga macrotrends ya baiyana yanayin rashin aikin yi a Najeriya daga shekara ta 1991 zuwa 2021. A cewar wannan rahoto, rashin aikin yi ya kasance a matsayin kashi 4.31 bisa 100.

Wasu bayanan kuma daga Statista sun nuna cewa tsakanin watanni uku na farko a shekarar ta 2015 rashin aikin yin na kan kashi 7.54 bisa 100, a watanni ukun da suka biyo bayan watannin farko kashi 8.19 bisa 100 sannan a watanni ukun da ke biye kasha 9.9 cikin 100, daga watanni ukun karshe kuma kashi 10.44 cikin 100 na al’ummar wadanda suka cike shekarun aiki wato tsakanin shekaru 15 zuwa 64 na haihuwa.

Domin tantance yawan marasa aikin yi, a kan duba yawan wadanda basu aikin a cikin rukunin masu shekarun aiki ne kawai, wato wadanda ke tsakanin shekaru 15 da 64 banda wadanda suka wuce ko wadanda ba su kai ba.

A watannin farko na 2015 adadin yawan masu aikin yi ya karu zuwa miliyan 73.4, daga miliyan 72.9 a watanni ukun karshe na 2014 wanda ya kasance kashi 0.69 cikin 100. Wannan na nufin cewa mutane 504,596 daga cikin rukunin mutan masu sekaru 15 – 64 suka sai aikin yi.

A daidai wannan lokacin kuma, adadin wadanda suke da aikin yi ya kasance a kashi 0.88 cikin 100 sannan kuma adadin wadanda suke aikin da suka sha karfin shi ya ragu da kashi 6.46 cikin 100 abun da ya rage adadin wadannan mutabeb daga miliyan 13.1 a watanni hudun karshe na shekarar 2014 zuwa 12.2

A waje guda kuma adadin marasa aikin yi ya karu da mutane 861,110 daga watanni karshe na shekara ta 2014 zuwa farkon 2015. A takaice akalla mutane miliyan 17.7 tsakanin shekarun 15 da 64 ne basu da aiki ko kuma suke aikin da suka fi karfi saboda karatun da suka yi ya wuce mukamin da suka samu.

Dubawa ta yi kokarin samun alkaluman marasa aiki a shekarar ta 2015 daga hukumar kididdiga ta kasa amma bamu samu ba. Sai dai na shekarun 2017 dana 2018.

A Karshe

Alkaluman da muka iya samu sun nuna cewa daga farkon shekarar 2015 kafin Buhari ya karbi ragamar mulki adadin marasa aikin yin na matsayin kashi 7.5 cikin 100 ne. Don haka zargin wai mutane miliyan 30 ne basu da aikin yi ba gaskiya bane.

Share.

game da Author