FARMAKIN BOKO HARAM KAN SOJOJI A MAINOK: Zulum na zargin makarkashiya kan kwace babbar tankar yaki daga hannun sojojin Najeriya

0

Gwamna Babagana Zulum na Jihar Barno, ya yi wa sojojin Najeriya nasiha cewa su rika sa tsoron Allah a zuciyar su, yayin tura wa sojojin da ke bakin daga manyan makamai.

Wannan nasiha ta Zulum alama ce da ke nuni da cewa akwai makarkashiya dangane da yadda Boko Haram su ka yi kwanton-bauna su ka afka wa sojojin Najeriya a Mainok, har su ka kwace wata babbar tankar yaki, mai iya tada gari da harbi daya.

A harin da Boko Haram su ka kai wa sojoji a Mainok, gari mai tazarar kilomita 55 daga Damaturu kafin a shiga Maiduguri, sun kashe soja har 18, kuma su ka kwace babbar tankar da aka kai wa sojojin kwana-kwanan nan daga Lagos.

Banda babbar tankar yakin, sun kuma kwshi manyan makamai a wurin.

Wata majiya abin dogaro ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa sabbin manyan makaman da aka kai wa sojojin da su ka hada da babbar tankar yaki samfurin T72, wato Giwa Bukkar Daji, duk Boko Haram sun kwashe su sun gudu.

Banda soja 18 da aka kashe, wasu 43 sun ji raunuka, a cikin wadannan sojoji na Bataliya ta Musamman ta 156 da ke Mainok.

Wakilin mu ya ji cewa Boko Haram sun kai harin ne kai tsaye domin kwatar manyan makaman da aka kai wa sojojin a ranar Juma’a.

Sun kai harin ne kwanaki biyu bayan kai manyan makaman.

“Maganar gaskiya abin nan akwai matukar takaici ainun a ce Boko Haram sun kwace Babbar Tankar Yaki T72, Giwa Bukkar Daji, wadda kwanan nan aka kai wa sojojin wadannan makaman.” Inji wata majiyar da har yau PREMIUM TIMES ba ta tantance lamarin ba.

Wasu majiyoyi sun ce hukumomin da ba na tsaron soja ba sun gargadi jami’an tsaro dangane da maharan, amma ba a yi komai ba, sojoji ba su maida martani da hanzari ba.

Sai dai kuma wasu majiyoyi sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa babu yadda za a yi a kai wa sojojin da aka kirke a Mainok hari, ba tare da wani dan cikin gida ya bada rahoton boye ga su Boko Haram ba.

Haka shi ma Zulum a sakon taya alhini da jimami ga sojojin Najeriya, ya yi zargin cewa akwai makarkashiya a cikin lamarin kisan da kai harin.

Ya na ganin akwai makarkashiya daga bangaren shugabannin da aka dora wa alhakin kai manyan makaman ga sojojin da ke bakin fama.

Sanarwar da Zulum ya fitar wadda ke dauke da sa hannun Isa Gusau Kakakin Yada Labarai na Gwamna, ya nuna cewa abin damuwa tare da bayyana cewa ba karamin cikas ba ne wannan hari da Boko Haram su ka kai wa sojojin da ke tsaron rayukan jama’a a kan hanyar Damaturu zuwa Maidugauri.

Sannan kuma ya mika sakn ta’aziyyar sag a iyalan sojojin da aka rasa.

Share.

game da Author