FANI KAYODE YA YI AMAI YA LASHE: Duk da kushe rigakafin Koronan Astrazeneca da ya rika yi ya garzaya an yi masa

0

Tsohon ministan sufurin jiragen saman Najeriya Femi Fani-Kayode ya yi allurar rigafin AstraZeneca na farko. Fani Kayode wanda ya dade yana nuna rashin gamsuwarsa da duk wata allurar rigakafin COVID-19 ya sanya hotonsa a shafin Twitter yayin da ake yi masa allurar.

Tsohon ministan ya ce allurar rigakafin da ake bayarwa a Najeriya ba na sannanen attajirin nan Bill Gates ba ne. Sannan ya ce akwai banbanci sosai tsakanin allurar da ake baiwa ‘yan Najeirya da wanda Hukumar Lafiya ta Duniya ke bayarwa. A cewar sa, ire-iren wadannan alluran da ake yi ne ya rika kushewa baya.

“Alluran rigakafin COVID-19 din da aka kawo Najeriya ba samfurin na Bill Gates ba ne, kuma ba wai an kokarin yin gwaji wani abu da mu bane . Wadannan an riga an yi musu gwaji mai nagarta, an tantance an kuma amince a bayar da su a duk kasashen duniya. Wannan daga kamfanin Oxford AstraZeneca ne” ya baiyana a shafinsa na twitter.

Kafin haka, a shekarar 2020, ranar 30 ga Afrilu, Fani Kayode ya yi gargadin amfani da duk wata allurar rigakafi ko maganin COVID-19 a shafinsa na twitter, inda ya jaddada cewa allurar za ta iya zama ajalin mutane.

A watan Mayun 2020, Fani-Kayode ya yi zargin cewa duk wata allurar rigakafin COVID-19 wani kullin makirce ne na Attajiri Bill Gates da matarsa Melinda su halaka mutane kawai. Ya kuma ce bugu da kari, wawa ne kawai zai yarda wai mutumin da ya yi imani da rage yawan al’ummar duniya zai fitar da allurar da za ta kare mutanen duniya.

Bill Gates na daya daga cikin mutanen da ke fuskantar kakkausar suka idan ana maganar abin da ya shafi allurar rigakafin COVID-19. Kama daga zargin cewa BillGates ya na wa ‘yan majalisar dokokin Najeriya tayin miliyan 10 na dalar Amurka zuwa inda ake zargin ya ce wajibi ne mutane akalla billiyan uku su mutu, da ma cewa shi ne sanadin barkewar annobar.

To sai dai duk wani yunkurin kirkiro allurar rigakafi tun daga 2020, hadin gwiwa ce tsakanin manyan kamfanonin magunguna na duniya da gwamnatocin kasashe.

Daga 18 ga watan Fabrairu 2021 allurai na rigakafi akalla guda bakwai aka kirkiro daga kamfanoni uku kuma har an kai su kasashe sama da 200 a yayinda wasu ke cigaba da yin gwajin na su inda har guda 60 sun kai matsayin a gwada a jikin mutane.

Ko akwai Allurar Rigakafi Mallakar Bill Gates?

Babu wata allurar rigakafi mallakar Bill Gates. Bisa bayanan da kasidar Lancet Journal ta wallafa, gidauniyar Bill da Melida gates sun yi alkawari kuma sun bayar da kudade wajen kirkiro allurai na rigakafi da suka hada da novavax, inovio, Dynavax SK Biosciences, Biological E da sauransu.

Ko Akwai allurar rigakafin da Hukumar Lafiya ta Duniya ke gudanar da bincike a kai?

Hukumar Lafiya ta Duniya ba ta da wata allurar da take turawa wata kasa. Saka ido da kuma tantance allurai don ganin ko suna da hadari, idan babu sai ta amince da amfani da shi.

Allurar AstraZeneca da Fani-Kayode ya yi yanzu a Najeriya daga COVAX ne.

Share.

game da Author