Fadar Shugaban Kasa ta caccaki Bishop Kukah kan ragargazar Buhari da ya yi

0

Fadar Shugaba Muhammadu Buhari ta zargi Babban Limanin Darikar Katolika na Sokoto, Bishop Mathew Hassan Kukah da cusa siyasa a sha’anin addini, inda ta ce kalaman Kukah kan Buhari ba furuci ce da ya kamata ya fito daga bakin malamin addini ba.

A cikin sakon Easter ne a ranar Lahadi Mathew Kukah ya kwankwatsi Buhari da gwamnatin sa, a kan yawan kashe-kashe da sauran matsalolin tsaron da ke addabar kasar nan.

Eater dai buki ne da Kiristoci ke yi a ranar Juma’ar farkon watan Afrilu, Lahadi da Litinin din farkon watan Afrilu.

Su na shirya bukin domin tuna ranar da Annabi Isa ya tashi, bayan kwanaki uku da ikirarin gicciye shi da Kiristoci ke yi cewa Yahudawa sun yi.

A cikin raddin da Fadar Shugaban Kasa ta maida wa Kukah, Kakakin Fadar Garba Shehu ya bayyana cewa “Kowane dan kasar nan ya na da irin na sa ra’ayin daban. Kuma kowa irin ta sa launin gaskiyar daban.

“To amma duk mutumin da ke ikirarin shi mutumin Allah ne, to kada ya bari ya cusa son zuciya da rashin adalci idan zai bayyana gaskiya.

“Furucin da ya yi cewa ta’adancin Boko Haram a yanzu ya fi muni fiye da kafin gwamnatin Buhari ta hau mulki cikin 2015, ba magana ba ce da ta kamata a ce ta fito daga bakin mai ikirarin cewa shi malamin addini ba ne. Saboda haka Kukah ya je Barno ko Adamawa ya tambaye su ko akwai bambanci tsakanin shekarar 2014 da shekarar 2021.”

Garba Shehu ya maida wa Kukah raddin cewa batun saka hijabi a Jihar Kwara kuwa, batu ne wanda kotun jiha ta bada hukunci. Kuma a wasu jihohi da dama tun zamanin mulkin Obasanjo ake fama da batutuwan, kuma babu inda sunan Buhari ya fito. Ko akwai ne? Inji Shehu.

“Kawai dai Kukah ya na cusa siyasa ne, kuma ya ke kokarin jan Shugaban Kasa cikin dagwalon siyasar da shi ya rigaya ya cambala kafar sa.

“Gwamnatin da ta kafa ma’aikata guda musamman domin kulawa da masu gudun hijirar da su ka rasa muhallin su, ba za a zarge ta da laifin yin watsi da wadannan masu gudun hijira ba, kamar yadda Kukah ya yi zargi.

“Wasu kalaman Kukah fa duk irin soki-burutsun da dama ya saba yi ne a duk inda a samu damar sakin bakin sa da bai iya yi wa linzamin da kamata malaman addini su rika yi wa harshen su.” Inji Garba Shehu.

A karshe Shehu ya roki jama’a su ci gaba da goyon bayan gwamnatin Buhari domin ganin an kawar da dukkan matsaloli da kalubalen tsaron da ke addabar kasar.

Share.

game da Author