Facebook da Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO sun kaddamar da sabon shiri na yaki da labaran karya game cutar Korona

0

Shafin sada zumunta na Facebook ya hada hannu da Hukumar Lafiya ta Duniya wajen kirkiro wasu matakai da zasu yi amfani wajen yaki da yada labarai marasa gaskiya game da cutar Korona a nahiyar Afirka.

Kamfanin APO group ya shaida hakan a madadin Facebook cikin wata sanarwar da ya wallafa ranar litini 5 ga watan Maris.

Za’a kaddamar da wannan hadin guiwa da aka yi wa taken “Mu hada kai don yaki da labaran karya game da cutar COVID-19” a harsuna biyu, wato Turanci da Faransanci a kasashen Afirka guda 10. Wadannan kasashe sun hada da Afirka ta Kudu, Zimbabwe, Zambia, Uganda, Kenya, Rwanda, Najeriya, Senegal, Cóte d’Ivoire da Jamhuriyar Dimokiradiyyar Kwango. Kamar yadda Kamfanin APO group ya shaida.

Tun da annobar Korona ta bullo, shafin facebook ya dukufa wajen ganin cewa mutane sun sami bayanai na gaskiya game da cutar. Dalilin haka kuwa shine don ayi wa mutane iyaka da labaran Karya da ake yadawa ya karade shafukan sada zumunta a musamman yanar gizo.

A watan Maris ne Facebook ya sanar cewa zai kaddamar da irin wannan shiri na yaki da ire-iren wadannan labarai da basu da tushe, mafi girma a duniya, inda zai rika samar da sahihan labarai game da maganin rigakafin Korona, wato COVID-19.

Sabon shirin wanda ya samu cikakken goyon bayan hukumar WHO za a rika samun sa ne a shafin Facebook. Tsarin wannan shiri shine, zai kunshi shawarwarin yadda mutum zai iya gano bayanai marasa gaskiya game da COVID-19.

Sanarwar ta kuma rawaito Aïda Ndiaye manajan kula da manufofin jama’a na cewa burinsu shi ne su tabbatar duk masu amfani da shafinsu sun sami bayanai masu nagarta dangane da allurar rigakafin Korona.

“ Za mu tabbatar cewa masu amfani da shafukanmu sun sami bayanai masu nagarta game da allurar rigakafin COVID-19. Wannan yana daga cikin aiyuka masu mahimmanci da muke yi a nan a Facebook. Daga nan har zuwa lokacin da za’a shawo kan cutar, za mu ci gaba da aiki da kwararru a fannin kiwon lafiya da jama’a a shafukanmu don ganin mun yaki bayanai marasa gaskiya mun kuma baiwa jama’a karin haske da za su taimaka musu wajen tantance duk wani abun da suka gani a yanar gizo. Wannan zai taimaka musu wajen yanke shawarar abin da za su karanta, wanda za su yarda da shi, da ma wanda za su yada,” a cewar Ndiaye.

Haka nan kuma, Facebook zai sake kaddamar da wani shafi na musamman wanda shi ma zai kasance a harsunan Turanci da Faransanci, kuma zai kunshi bayanai kan duk matakan da yake dauka don yaki da bayanan marasa gaskiya.

A cewar Facebook wannan zai kara bayyana sahihanci dabarunsu na fadakar da al’umma da ma irin matakan da su ke dauka wajen yaki da bayanan karya game da batutuwa masu daukar hankali a duniya kamar COVID-19 da zabe da sauyin yanayi.

Share.

game da Author