A yau Asabar ne a gwabza tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da Real Madrid a Madrid.
An doka kwallo sai dai an yi zargin Referee da murde wa kungiyar Barcelona da ni kwallon wanda da ya hura usur da an buga daga kai sai gola.
Ana ganin da alkalin wasa ya hura wannan fizgar Braithwaith da Mendy na Madrid yayi da shike nan an buga kunnen doki, sai dai kash abin bai yi haka ba.
Madrid ce ta yi nasara a wasan duk da Barcelona ce ta fi yawan kai farmaki da taka leda a wasan sai dai kash, kwallaye sun ki shiga raga.
Babu kamar a mintin karshe na lokaci da aka kara inda kamar zata shiga raga amma inaaa.
Yanzu dai Madrid ta dare saman Tebur a Laliga.