A wasan dare na El-Clasico da ya gudana ranar Asabar tsakanin Real Madrid da abokiyar adawa kuma abokiyar gabar ta Barcelona, kungiyoyin biyu na Spain sun buga abin da su ka saba, wato wasan kwallon da a kowane lokacin karawar su, duniya ke kagara ranar karawar ta zo, domin kowa ya kashe kwarkwatar idon sa.
Sai dai kuma wadanda su ka maida hankali a kan fitaccen dan wasan Barcelona, Leonel Messi, a wannan karon ma sun kwashi buhun kunya.
Dalili, an shafe wasanni bakwai kenan na El-Clasico bayan tafiyar Cristiano Ronaldo zuwa kungiyar Juventus ta birnin Turin da ke Italy, amma tsawon wasanni 7 ba aka yi tsakanin Marid da Barcelona, Messi bai sake samun nasarar jefa kwallo a ragar Madrid ba.
Sannan kuma wasanni uku na El-Clasico da aka buga cikin wannan shekara daya a jere, duk Madrid ce ke yin nasara a kan Barcelona, gida-da-waje.
A na sa bangaren, tun da kociyan Madrid Zinedine Zidane ya je kulob din, ya sace karfin iskan tayar Barcelona sosai, ta yadda ya dauki kofin Champions’ League sau uku a jere, a kan idon Barcelona.
Sannan kuma sau da yawa idan an yi arangama tsakanin kungiyoyin biyu, Barcelona ce ta fi shan dukan tsiya.
Ko a wasan farko na La Liga da aka buga a Camp Nou, Madrid ta yi wa Barcelona dukan tsiya da ci 3:1, kafin a buga wasa na biyu da aka yi jiya Asabar, inda Barcelona ta kara shan duka da ci 2:1.
Messi Ya Yi Kyarmar Sanyi:
A wasan da aka yi jiya a karamin filin Madrid, bayan an dawo hutun rabin lokacin, ruwan sama mai karfi ya goce, har aka nuno Messi ya na makyarkyatar jin sanyi. Wannan ya kai ga Messi ya nemi a canja masa wata rigar da ya ke wasa da ita.
Madrid ta buga wasa a ranar Asabar ba tare da fitattun ‘yan wasan ta da su ka ji rauni su uku ba, wato Sergio Ramos, Raphael Varane da Dani Carvajal. Sannan kuma a bayan an kusa tashi wasan, an daga wa Casemero jan kati, abin da ya jawo Madrid ta karasa wasan da ‘yan wasa 10.
Kana kuma dan wasan ta Varquez ta ji raunin da a yau Lahadi aka yi sanarwa cewa ba zai sake buga wasa ba har karshen wannan kakar La Liga da ta rage saura wasanni takwas a kammala.
Ganin babu gogaggun ‘yan bayan Madrid, irin su Ramos da Varane a wasan bai sa Messi ya yi bajintar jefa kwallo a ragar Madrid ba.
Shi ne fa masu kallon kwallo ke tambayar ko dai ‘ta fara kare wa Messi ne?