Duk macen da ba ta iya ladabtar da mijinta da girki mai lagwada ba, bata cika mace ba – Jarumi

0

Fitaccen jarumin finafinan Najeriya, Pete Edoche ya bayyana cewa rashin kun ya da tsagalgalewa, zazzare idanu da ‘yancin mata da ake rudan mata da shi ne ya sa suke shan dan karan duka a gidajen auren su.

A hira da yayi da BBC Igbo, Edoche ya ce ” Wai ‘Yancin mata da rashin kun ya na zamani shine ya ke rudin matan yanzu. Sai kaga zankaleliyar mata wai bata iya ta girka wa mijinta abinci mai dadi ba.

” Duk macen da bata iya ladabtar da mijinta da girki ba, ba ta cika mace ba. Kamata yayi idan maigidanki ya dawo, girkin matarsa ya natsar da shi, ya rika rige-rigen dawowa gida ya kwashi girki, ba irin matan yanzu ba da suka lalace da wani abi wai yancin mata, da rashin kuya.

Amma matan yanzu ba su iya girki ba suna can suna watangaririya wai su yancin mata.

” Duk matan da zata canja sunanta ko kuma ta ruka hadawa da na mijinta ya kamata ta san cewa wannan mutum yana da daraja a rayuwarta.

Shekara ta 52 a aure sannan yaya na 5 dukkan su da mata, da ni da su babu wanda ya taba daga hannun sa ya dalla wa matarsa mari.

A karshe ya hori mata da suyi koyi da halayen iyayen mu da yadda suka daraja iyayen mu maza.

” A loka in ina yaro, mahaifina Allah-Allah ya ke ya dawo gida ya kwashi girkin maman mu.

Share.

game da Author