Dole A Dakatar da Kashe Ƴan Arewa a Kudu -Gwamna Matawalle

0

Ya zama dole a matsayina na gwamna kuma mai kishin Arewa da nayi magana akan abubuwan dasu ke faruwa a kasar nan. Wannan ba magana ce ta siyasa ba. Lokaci yayi da zamu faɗawa kanmu gaskiya domin dawwamar zaman lafiya da cigaban ƙasarmu, da kuma kare Najeriya daga afwaka tashin hankalin da wasu ɓata-gari ke son jefa ta a ciki.

Duba da yadda mukeyin siyasa a ƙasar nan, za ayi tsammanin jawabi irin wannan daga gwamna ko wani shugaba na jam’iyar APC zai fito, ba ni ba cikakken ɗan jam’iyar adawa ta PDP. Na yanke shawarar yin wannan jawabi ne saboda kishin Najeriya tare da neman wanzar da zaman lafiya da cigaban Arewa.

Abubuwa da dama, marasa daɗi, na faruwa ga Arewa da kuma mutanen Arewa. A kullum ana kashe ƴan Arewa, ana lalata dukiyoyinsu a wasu sassa na Kudancin ƙasar nan duk da ƙoƙarin da shugabannin Arewa keyi na kwantar da hankalin mutanensu, da kare mutunci da rayuka, da dukiyoyin d ‘yan Kudancin Najeriya mazauna Arewa.

Duk da irin mawuyacin halin da ‘yan Arewa suka samu kansu musamman a  Kudu maso Yamma da Kudu maso Gabas, shugabanni da manyan mutane ƴan Arewa sunyi shiru. Maimakon su marawa yankinsu da jama’arsu baya sunyi tsit, saɓanin mutanen Kudu wanda ke kare mutanensu koda kuwa basu da gaskiya.

Shiru da shuwagabanin Arewa sukayi duk da tsangwamar mutanensu da akeyi domin tabbatar da zaman lafiya a ƙasa ba tsoro bane. Ko wace alumma zata iya dukkan abin da yakamata domin kare kanta in hakan ya zama dole. In dai ba za a tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan Arewa a Kudancin Najeriya ba, to kada ayi tsammanin Arewa zata kare ‘yan Kudu mazauna Arewa. 

A kwanakin baya an kashe ‘yan Arewa, aka ƙona dukiyoyinsu a kasuwar Sasa. Anyi hasara mai ɗumbin yawa, amma shuwagabannin Yarabawa basu yi komai ba a kai, sai ma kare miyagun da sukayi wannan ta’asa da sukayi. Wasun su ma cewa sukayi lefin mutanen Arewa ne.
 
Biyo bayan kisan da aka yiwa ‘yan Arewa a jihar Imo ranar Lahadin data gabata, ya zama dole ayi Allah-wadai da kisan gilla da ƙiyayyar da ake nunawa ‘yan Arewa a Kudancin ƙasar nan. Ba zamu ƙara yadda a kashe mana mutane ba. Ko wane ɗan Najeriya yana da damar yin kasuwanci a ko ina.

‘Yan Kudu na da tarin dukiya a Arewa fiye da ‘yan Arewa ke dashi a Kudanci ƙasar nan, amma babu wanda yake musu barazana.  A ko yaushe muna ƙoƙarin wanzar da zaman lafiya. In aka yi duba na tsanaki akan rahotannin  farmakin da ake kaiwa ‘yan Arewa a Kudancin Najeriya, za a gane masu son zaman lafiya, da waɗanda burinsu ta da hankali to tunzura mutanensu.

Kowa ya san su waye ‘yan iskan da suke kai farmaki (kan ‘yan Arewa), da waɗanda ke ɗaukar nauyinsu. Mun san masu yaɗa ƙiyayya, da masu tada tarzoma. Amma abun takaici sun hana gwamnatin Tarayya ɗaukar wani mataki akan haka; gwamnati ta zuba musu ido suna cin karen su babu babbaka. Najeriya ƙasa ɗaya ce. Duk wanda baya son cigaba da zamanta a dunƙule, yana da damar ƙalubalantar tsarin mulki na ƙasar, ko kuma ya tattara ya bar ƙasar, amma ba ya riƙa yiwa was ƴan ƙasa barazana ba.

A matsayina na gwamnan jam’iyar PDP, ban yadda da siyasa ta ko-a-mutu-ko-ai-rai ba. Neman muƙami ba zaya hanamu faɗin gaskiya ba, ko goyon bayan mutanenmu yayin da ake takalarsu da faɗa.
 
A matsayina na ɗan Arewa, ina Allah wadai da yadda wasu suke cin mutuncin shugaba Buhari kuma suna nuna ƙiyayya a fili ga Arewacin Najeriya da sunan zanga-zanga. Duk irin ƙorafin da suke dashi, ba hujja bane abinda su kayi. Abinda su kayi tsagoron jahilci ne, kuma ɓatanci ne ga Shugaban Ƙasa. Wannan na tabbatar da irin ƙiyayyar da ake nunawa Arewa. Zagin Shugaban Ƙasa ba shi ne hanyar isar da ƙorafi ba. Zagin Shugaban Ƙasa ƙasƙanci ne da nuna ƙiyayya, kuma shiri ne na Kudancin Najeriya, domin kuwa mun san wadanda suka yi zagin da masu ɗaukar nauyinsu. Doka ta amince da zanga-zanga ta lumana, amma amfani da zanga-zanga don cin mutuncin Shugaban kasa, iyalinsa ko iyayensa (kamar yadda ya faru a Landan) abin takaici ne, abin Allah-wadarai ne.  Da Buhari ɗan Kudu ne, tabbas baza su yi masa haka ba. Makasudin yin zanga-zangar shine muzanta Shugaban Ƙasa. Wannan yasa idan aka duba za a ga cewa masu zanga-zangar ‘yan tsirarai ne, in aka yi la’akari da yawan ‘yan Najeriya mazauna birnin Landan
 
Idan Arewa na son cigabanta, ya zama dole ta kare kanta, kuma dole shugabanni su jajirce wajen kare Arewa kamar, ko fiye ma da yadda ‘yan Kudu su keyi, a duk lokacin da aka taɓa musu mutum ko wani abu. Kada mu ji kunyar kare mutuncinmu kamar yadda abokan zamanmu keyi. Amma kada mu kare laifukan mu (kamar yadda suke yi). Najeriya ƙasar mu ce gaba ɗaya. Dole kowane ɗan Najeriya yayi ƙoƙarin dauwamar da zaman lafiya. Dole a kare mutanenmu a Kudu a jiki, kamar yadda mu ke jan mutanen Kudu a nan Arewa. Muna fata tare da jankalin mutanenmu da su zauna lafiiya domin zaman lafiyar su a wajen shi zai

Sa hannu:
Alhaji Dr. Bello Mohammed
(Matawallen Maradun),
Mai girma GwamnanJihar Zamfara

Share.

game da Author