Idan ba a manta ba, dan bindigan da ya shirya kuma ya jagoranci sace daliban makarantar sakabdaren Kankara Awwal Daudawa ya mika kai inda ya mika makaman sa, akalla bindigogi kirar AK-47 20 tare da wasu makarrabansa 5.
Daily Trust ce ta yi hira da Daudawa a wancan lokaci inda ya ke bayyana cewa yayi na’am da sulhu kuma ya yarda ya ajiye makamanta ya tuba.
Sai dai kuma ko cikakken wata uku ba a yi ba, sai gashi jaridar ta sake ruwaito wa cewa wannan gogarman masu garkuwa da mutane, wato Daudwa ya koma ruwa.
Ya tattara iyalan sa sun fice daga gidan da gwamnati ta siya masa a Zamfara bayan ya tuba, ya kira makarraban sa, sun kwashi makamai sun nausa daji ci gaba da sana’a.
Da ya tabbata ya natsu a daji, sai ya kira wani makusancinsa a Gusau ya shaida masa cewa, yanzu fa ya koma daji, sai wada hali ta yi.
Ko a lokacin da aka yi sulhu da Daudawa, an yi masa alkawarin gida, kuma an siya masa gidan, saidai kuma akwai yiwuwar wasu daga cikin manyan alkawuran da aka yi masa ne, ba a cika su ba.
Wani shugaban masu garkuwa da mutane a jihar Zamfara Shehu Rekeb, ya shaida wa Daily Trust cewa, wannan ma somin tabi ne, sauran wadanda suka ajiye makamai a baya duk za su koma ruwa, saboda gwamnati bata cika alkawuran da ta dauka ba.
Wani jami’in tsaro da aka tattauna da shi ya bayyana cewa dama irin wannan yarjejeniyar yana rushewa, domin babu wata takarda da aka saka hannu akai, sannan babu wani shiri na yadda za a gyara halayen su da kuma fadakar dasu muhimmancin yin sulhu da sauransu.
Discussion about this post