Dalilin da ya sa na shirya gangamin yi wa Buhari zanga-zanga a Landan – Reno Omokri

0

Reno Omokri ya bayyana cewa “na garzaya Landan a ranar 2 Ga Afrilu, 2021 domin jagorantar zanga-zangar tilasta wa Shugaba Buhari komawa gida Najeriya (#HarassBuhariOutOfLondon), kuma daga filin jirgi na zarce kai-tsaye wurin zanga-zangar.

“Ban yi barci ba, ban huta ba, kai ko wanka ban tsaya na yi ba. Hadiman Shugaban Kasa su ka turo min ‘yan sandan Landan, su ka rufe ni da tambayoyi. Amma a karshe, su ka bayyana da bakin su cewa ban aikata wani laifin da za su kama ni ba. Kuma zanga-zangar da mu ke yi ba ta kauce ka’ida ba, ta lumana ce kuma dokar kasar ta ba mu iznin yin zanga-zangar.

Yayin da hadiman Buhari su ka turo min dan sanda, sai na tsaya a natse na yi masa wadannan tambayoyin ni ma, kuma an nuno mu kai-tsaye duk duniya an gani:

“Yallabai, shin Mai Alfama Sarauniyar Ingila Elizabeth II ta taba zuwa Najeriya neman magani a asibitin mu? To saboda da me za a turo ka ka tambaye ni don na zo na ce shugaban mu ya koma kasar sa ya nemi magani a can cikin asibitocin mu?

“Daga nan dan sandan ya yi lakwas, ya ce mu na da ‘yancin yin zanga-zanga. Kuma ya jinjina min babban yatsan sa, ya kyale mu mu ka ci gaba da zanga-zangar mu.”

“Batun dalilin da ya sa na shirya zanga-zanga kuwa, saboda na yi amanna cewa Buhari ba gwamnati ce ya ke tafiyarwa ba. Kawai dai ya na jagorantar wani gungun mabarnata ne.

“Buhari ya shafe sama da shekaru biyar a kan mulki. An ware sama da naira biliyan 10 wajen samar da magani a asibitin cikin Fadar Shugaban Kasa. Kusan dala milyan 27 kenan. wadannan kudade sun isa a gina asibitoci a dauki ma’aikata a Najeriya, shi da sauran jama’a su rika zuwa ganin likita. Amma matar sa da kan ta ta bayyana cewa ko paracetamol da sirinjin allura babu a asibitin.” Inji Omokri

Omokri ya kara da cewa har akwai dalilin rufa-rufar da aka yi wajen kashe masu zanga-zangar #EndSARS a Lekki, shi ma ya sa sun shirya wa Buhari zanga-zanga a Landan.

Ya ce Amerika ta kasa gano hakikanin gaskiyar kisan da aka yi, saboda gwamnatin Najeriya ta boye mata gaskiyar llamari, kuma ta binne hujjojin da za su iya tabbatar wa Amurka an kashe masu zanga-zanga a Lekki.

Reno ya ce kwata-kwata zanga-zanga ba ta da wata alaka da kabilanci, domin shi kan sa ai ya goyi bayan marigayi Umaru Yar’Adua da Atiku, wadanda dukkan su Fulani ne kamar Buhari.

“Har ma gara Atiku shi ne cikakken Fulani, domin shi Buhari ko yaren Fulatancin ma ba ya ji.”

A karshe Omokri ya ce wayewar Buhari kadan ta dara wayewar ‘yan bindigar da ke addabar kasar nan.

Share.

game da Author