Buhari ya gaggauta saka dokar ta baci a fannin tsaron kasar nan, harkar tsaro ta dagule – ‘Yan Majalisa

0

Majalisar Tarayya ta yi kira ga Buhari da kakkausar murya cewa lallai ya saka dokar ta baci a fannin tsaron kasar nan.

Mambobin majalisar da suka tofa albarkacin bakunan su a zauren majalisa a lokacin da ake muhawara akan matsalolin tsaro da suka kunno kai a kasar nan, sun bayyana rashin jin dadin su kan yadda gwamnatin tarayya ta ke riko sakainar kashi da matsalar tsaro a kasar nan.

Kusan babu wani yanki a fadin kasarna da ba aya cikin tsananin razhin tsaro a kasar nan.

‘Yan majalisan sun gargadi Buhari da ya gaggauta saka dokar ta baci domin matsalar rashin tsaro ya wuce gona da iri.

A majaisar Dattawa ma sanatoci sun yi irin wannan muhawara.

Sanata Smart Adeyemi, wanda ya barke da kuka a lokacin da yake jawabi, ya yi kira ga sanatocin da su cire siyasa kowa ya tattaro hankalin sa wuri daya a sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari halin da kasa ke ciki.

” Gaskiyar magana shine Najeriya ta shiga halin kakaknikayi game da matsalar rashin tsaro wanda bata taba fadawa ciki ba. Wannan matsala fa ya kai intaha, dole mu ajiye siyasa a gefe mu fada wa kan mu gaskiya. Ko ina ya dagule, babu tsaro.

” Yau mutum bashi da damar yin tafiya a Najeriya, ko ina ana cikin matsala na tsaro. Ina zamu saka kan mu. Abu ya kai ga hatta ana kakkafa tutoci a wasu ya kunan kasar nan.

Sanata Adeyemi Smart, a karshe dai sai da ya barke da kuka, ya rika zubda hawaye kafin ya kammala jawabin sa.

Sannan kuma ya ce idan taimako ne Najeriya ke bukata, ta garzaya waje ta nemo mana.

Share.

game da Author