Buhari na baiwa ‘yan uwansa Fulani bindigogi su kashe mu, mu kuma ya hana mu – Gwamna Ortom

0

Gwamnan jihar Benuwai, Emmanuel Ortom ya zargi shugaban kasa Muhammaxu Buhari da rabawa wa Fulani makamai su yake su a jihar Benuwai, sannan kuma shi ya hana su mallakar makamai su kare kan su.

Ortom cikin kakkausar murya ya bayyawa wa dandazon mutabe da suka tare hanyar a Bebuwai bayan kisan wasu da ya ce wai Fulani ne suka aikata ya ce tura fa ta kai bango.

” Abinda ke faruwa yanzu ya nuna cewa babu shugaban kasa a kasar nan, gaba daya komai ya dagule, Buhari yana kare yan uwan sa Fulani sannan ya na dirka musu makamai su ya ke mu amma kuma ya hana mu mallaki bindigogi mu kare kanmu.

” Ga ba daya mulki ta subuce daga hannun Buhari, babu abinda ya ke iya yi, yau ya ce kaza, ministan sa ya fito ya canja kuma babu abinda zai faru. Buhari na mara wa Fulani baya su kwace kasar nan gaba daya. Wannnan shine gaskiyar magana.

A jawabin da yayi, Ortom ya jaddada cewa tura fa ta kai bango yanzu, tunda dai da alamar babu shugaba a kasar nan kowa yana yin abinda ya ga dama sannan Buhari na basu kariya.

” Idan da gaske ne, me ya sa Buhari ba zai saka a cafke shugabannin Miyetti Allah ba, tun da na gano sun yi ganawa da yan uwansu daga kasashe 13, cewa sai sun ga bayan jihar Benuwai, kuma ya sani amma an barsu sabo yan uwan shi ne.

Share.

game da Author